Sheikh Bashir Lawal ya fara karanta raddin littafin “Lillahi thumma lit tarikh

Sheikh Bashir Lawal ya fara karanta raddin littafin “Lillahi thumma lit tarikh

A ranar lahadin da ta gabata ne Sheikh Bashir Lawal ya fara karanta raddin littafin “lillahi thumma lit tarikh” a makarantar Hauzatu Baqiril Ulum Kano wadda take karkashin kungiyar Shi’a ta Rasulul A’azam.

Daga cikin dalilan da suka sanya malamin ya kudiri aniyar karanta raddin littafin shine wai sun samu labarin wani Malamin wahabiyawa a Kaduna mai suna Sheikh Khamis Al-Misriy yana karanta littafin domin batanci ga Shi’a,shi yasa ya ga dacewar karanta raddin littafin domin warware shubhohin littafin da samun zaman lafiya a cikin al’umma.
Sheikh Bashir ya fara da karanto irin sharrace sharrace da kage-kage da ake  cikin wannan littafi.Yana cewa:
  “Zaka ji suna cewa dan shi’a in zai tafi unguwa sai ya samu amininsa ya damka masa matarsa yace ga ta nan in tana da bugata na sha’awa ya cigaba da biya mata.
  “Wani abu wanda duniyar kafirci ba a taba ji ba,amma mutanen nan saboda hiqdi da wani irin mugun kulli da suke wa addinin musulunci,ko me Annabi Muhammadu yayi masu?suka nuna shine bai iya tarbiyyan al’umma ba a cikin al’ummar sa masu sallah suke wannan.Ba mu taba jin wannan ya faru hatta a Isra’ila ba,ba mu taba jin wannan ya faru hatta a Amerika ba.
  “Abin takaici zaka samu wawaye masu karamar kwalkwalwa wahabiyawa suna gasgata wannan.Zaka ji ana tambayan matayen mu wai da gaske ne?Allah yana cewa: “IN JA’AKUM FASIQUN BINABA’IN FATABAYYANU AN TUSIBU QAIMAN BI JAHALATAN ….”Akwai fasiqancin da ya fi irin furta wannan kalma da tuhuma da kage ma al’ummar Annabi?
“Ko a ce suna yin mut’a da yarinya ‘yar shekara hudu.Wai zaka ga dattijo dan shekara 70 yana mata fyade.Duk duniya in  ka bincika wannan babu,amma saboda shegantaka al’ummar shi’a ake ma irin wannan kazafin.”
Malamin ya nuna cewa a duk lokacin da makiya suka tsananta wajen fada da shi’a da kage da sharri,to,a lokacin ne kuma mutane suke fahimtar shi’a din,saboda ko shi ma malamin ya nuna a lokacin da Shugaba Regan na Amerika ya tsananta fada da Imam Khomaini da Iran a lokacin suka fahimci shi’a din duk da sharri da kage da ake ma shi’a din.288

comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.