Raddin Littafin “Lillahi Thumma Lit Tarikh - Kashi Na Biyu- Na Shekh Bashir Lawal

Raddin Littafin “Lillahi Thumma Lit Tarikh - Kashi Na Biyu- Na Shekh Bashir Lawal

Idan aka yi dubi zuwa ga wanda ya rubuta littafin “lillahi thumma lit tarikh” da abubuwan dake cikin littafin za a fahimta akan marubucin littafin Bawahabiye ne

A Ranar Lahadi,30 ga watan Yuli 2017,Sheikh Bashir Lawal a lokacin da yake cigaba da karanta raddin littafin “lillahi thumma lit tarikh” a makarantar Hauzar Baqirul Ulum dake Kano,ya bayyana cewa in da a ce mutum zai dubi da kyau zuwa ga marubucin littafin “lillahi thumma lit tarikh” da abubuwa dake cikin littafin zata bayyanawa mutum cewa lallai marubucin ba dan shi’a bane,Bawahabiye ne,shi yasa ma da kanshi yace ba sunan da ya ba kanshi a littafin bane sunan shi, “isti’ara” ne, wai saboda ka da ‘yan shi’a su gane shi su kashe shi.
Sheikh Bashir ya bayyana cewa a wannan raddin da zai dinga yi zai yi kokari ya shakkasa su waye ‘yan shi’a,sannan kuma zai yi bayanin su waye wahabiyawa.Saboda haka kada wani yayi tunanin da shi yake yi,yana yi ne da wa’yannan mutanen da suke karanta littafin domin batanci ga shi’anci da akidunta.
Malamin yana cewa :
  “….Su wa’yannan mutanen zaka ga sauti daya na ‘yan shi’a na firgita su.Ba sa so a saurare ka,su zasu fadi yanda kake,sannan kuma su dinga yin raddi akan sunan naka da akidunka.Ba za su bar jama’a su ji sunan ka da kanka ba,wato kai kayi bayanin sunanka da kanka ba.Wannan daya ne daga cikin “asalib” dinsu wanda zamu gani.Wannan ne ya sa mu zamu ce mu ‘yan shi’a ne Imamiyyah wa’yanda ke bin Imamai sha biyu,wa’yanda makarantun mu na shi’a sanannu ne.Najaf tana daga ciki,Qum tana ciki,sannan akwai ta Siriya,akwai ta Lebnon,akwai ta Kuwait,akwai hauzozin ilimi a kasashe da daman a musulmi.
Ya cigaba da cewa:
  “…Idan da bamu da samuwa,ana iya amfani da bakinmu a ci mana albasa,Alhamdulillahi yanzu akwai mu.A zuwa yanzu malunta da kololuwanta bamu fara samu ba a Nigeriya,muna fata nan ba da dadewa ba za a samu,saboda maluntan a duniyar shi’a kaman yadda mun sha fada a karatuka na tana farawa ne daga ijtihadi.To amma akwai dalibai,kuma Imam Sadiq yace daman dalibanmu sunfi malamansu.To,mu dalibai ne,har yanzu muna nan muna dalibta ne.
“To,mu ‘yan shi’a ne Isna ashar,kuma wa’yanda muke ma raddi sune ‘yan salafiyya,wa’yanda suna da sunaye a Nigeriya a cikin sunayensu akwai “Izalatul bid’a wa iqamatus sunnah”,sannan ‘yan izalan suna kashi kashi amma mafi yawansu sun hadu akan akida daya.Saidai akwai wa’yanda kaman yanda na ji Sidi Musal kasiyuni ne a daya daga cikin bayanansa cewa kafi izala,sune wa’yannan din.
  “Wani lokacin suna kan gaba gaba,saboda ‘yan izala na gargajiya akwai inda suke tsayawa,a cikinsu akan samu wasu mukhlisai.Ka ga basa iya maka sharri,amma ‘yan kafi Izala su sun wuce wannan,suna sharri da kage,zasu iya amfani da kowacce kalma wajen ambatonka.”
Malamin ya fara karatun raddin littafin na “lillahi thumma lit tarikh” da ta’arifin shi wanda ya rubuta littafin na “lillahi thumma lit tarikh”.Yana cewa:
  “Hakika marubucin shi wannan littafi na “lillahi thumma lit tarikh” a bugun farko shafi na 104 cewa sunan da aka rubuta a bangon littafin Sayyid Husain Musawiy ba sunansa na yanka bane,suna ne da  ya aro.Yai bayanin sababin da yasa ya boye sunansa,wai yana tsoro kada lamarinsa ya bayyana a san shi,a aiwatar da abinda ba a godewa karshensa ya faru-menene abinda ba a godema karshensa ya faru?Shahada ce ba ya so?Kuma a ina dan shi’a ya zama dan ta’adda kaman shi?Dan shi’a ya saba tattaunawa ne.A ina ne dan shi’a yake fada da mukalafi yake amfani da makami,ya tilastaka ya hana ka bayyana ra’ayinka?a duniyar shi’a babu wannan.To,shi dai ya fadi haka nan.
  “Tare da cewa marubucin a muqaddimarshi yana cewa shi mutumin karbala ne-Sayyid Kamal Hayadri shima mutumin Karbala ne,Karbala ta fitar da manya manyan malamai sanannu.Kuma wai ya samu darajar Ijtihadi da yabo mai girma-shi ya dauka ijtihadi jawabawa ce ta Academic ne na doktora ne sai a rubuta maka maki a ce ka samu dari bisa dari ko abinda yayi kama da wannan.Wanda maganganusa duk dan shi’a zai masa dariya.Kalmar Ijtihadi ba harka ce ta jarabawa irin wanda kake shiga aji ka zauna ba,a’a,malami zai gwada ka ne bayan ka mallaki dukkan ka’idoji na ilimi sai a kirkiri maka wata mas’ala wacce ba  ta da samuwa,wato babu wani malamin fiqhu da yai rubutu akanta,sai a kirdadota a ce da irin wannan mas’alar zata faru menene?,shigen ace misali da a ce ilimi ya wadatu sai ace kirkiran maniyyi daga ‘ya’yan itace,kuma a kirkiri yanayi na mahaifa sana’I,a samu kwayoyin halitta a kirkira wa’yanda zasu iya zama kwai,a samu wannan a hada shi a ciki sai ya fitar da da.To,wannan dan yaya hukuncin sa?Ya zai kasance?Ire iren wa’yannan abubuwan iftiradiyyat kilan babu su a duniya,basu samu ba tukuna….”
Malamin ya kawo dalilai masu yawa akan cewa shi wannan marubucin ba dan Shi'a bane kuma bai yi karatu a makarantun shi'a ba.
Domin samun cikakken jawabin kuna iya neman karatun malamin na ranar lahadi 30 ga watan yuli 2017

comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.