Daawar Karya Ta Mahadiyyanci

Daawar Karya Ta Mahadiyyanci

Related Articles

Imam zaman (imam Mahadi) (A.S) a wasikar karshe da ya aikawa wakilinsa na hudu ya bayyana cewa: Kai mai mutuwa ne nan da kwana shida, ka shirya al'amuranka, kuma kada ka yi wa kowa wasiyya game da mai maye gurbinka, lokacin boyuwa cikakkiya ya yi… kuma a nan gaba wasu daga shi'a na zasu yi da'awar ganina, Ku sani duk wanda ya yi da'awar ganina daga shi'ata kafin bayyanar Sufyani da tsawa to makaryaci ne[1]!

Da wannan bayani ya bayyana a fili cewa duk wani Shi'a ya san aikinsa, masu da'awar alaka da imam Mahadi (A.S) da da'awar wakilci na musamman daga imam Mahadi (A.S) to sun zama makaryata.

Wasu ma suna wuce gona da iri ne, bayan sun yi da'awar wakilci daga nan kuma sai su yi da'awar su ne imam Mahadi (A.S), daga nan sai su kafa mazhabobin bata da barna da karkatar da akidun mutane daga imani na gaskiya zuwa ga bata[2], wadannan irin kungiyoyi idan mai bincike ya koma tarihi zai gan su, kuma yawancinsu sun samu goyon baya daga 'yan mulkin mallaka ne.

A fili yake cewa wadannan kugiyoyin na bata da kuma mutane masu da'awar mahadiyyanci ko kuma wakilcin imam Mahadi (A.S) al'amarinsu tun farko yana da nasaba da jahilcinsu. Wasu kuma tsananin son su hadu da imam (A.S) da karancin saninsu da imam da shi, da gafala daga samuwar makaryata sai ya sanya su fadawa irin wadannan tarkuna na makaryatan mutane.

Don haka shi'a dole ne ya kasance yana da ilimi isasshe game da sanin imam Mahadi (A.S) domin kada su fada tarkon mayaudara da makaryata masu batarwa, kuma su lizimci biyayya ga malamansu a kan tafarkin tsira da hasken shiriya.

 

 

 

[1] Kamaluddin, j 2, babi 45, h 45, shafi: 294.

[2] Kamar: "Babiyya" ta "Ali Muhammad Bab" da ya yi da'awar wakilcin imam Mahadi (A.S), sannan sai kuma ya yi da'awar shi ne Mahadi, sannan kuma ya yi da'awar annabta, ya kafa kungiya mai batar da mutane ta Baha'iyya.

 


comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.