Bincike kan Imam Mahadi a.s

Bincike kan Imam Mahadi a.s

Related Articles

Game da amsar wannan magana za a iya cewa, bincike game da mahadiyanci yana daga mudu’ai da suke su ne sirrin mabudin rayuwar dan Adam kuma suna da alaka ta kai tsaye ga rayuwar mutum. Saboda haka duk da kokarin da aka samu a wannan fage, amma akwai abubuwa da yawa da suke ba a yi bincike game da su ba, kuma malamai da marubuta ba su yi wani kokarin a zo a gani ba a wannan fage.

Domin sanin tilasci da wajabcin bincike game da imam Mahadi (A.S) bari mu duba wadannan bayanai masu zuwa:

1- Bincike game da imam Mahadi yana komawa zuwa ga mas’alar imamanci ne wacce take daya daga asasin akida gun Shi’a imamiyya kuma bayanai masu fadi na asasi sun zo a kan hakan a cikin Kur'ani mai girma da sunnar annabi (S.A.W).

Shi’a da Ahlussunna duka sun ruwaito daga Annabin rahama (S.A.W) da cewa:

“Duk wanda ya mutu bai san imamin zamaninsa ba to ya yi mutuwar jahiliyya”[1].

Saboda Allah, shin abin da yake ya shafi dukkan rayuwar mutum ta lahira kai tsaye bai dace ya samu kula da la’akari na musamman ba?

2- Imam Mahadi (A.S) shi ne na goma sha biyu a salsalar sarkar gidan tsarki da imamanci, wanda shi ne daya daga cikin abubuwan da annabi (S.A.W) ya bar mana a matsayin wasiyya, wanda aka karbo a wata ruwaya daga annabi cewa: “Ni na bar muku nauyaya biyu littafin Allah da Ahlin gidana; ba zaku taba bata ba har abada matukar kun yi riko da su…”[2].

Saboda haka ne bayan Kur'ani mai girma wanda yake maganar Allah ne, wace hanya ce tafi ta mas'alar imami (A.S) bayyana karara da shiryarwa. Shin tun farko ma kur’anin Allah zai iya fassaruwa da bayyanuwa ba tare da bayanin halifan Manzon Allah ba mai maye gurbinsa?

3-Imam Mahadi (A.S) imami ne wanda yake rayayye kuma mai duba zuwa garemu, kuma da akwai tambayoyi masu yawa da suka rage -musamman tsakanin samari- da ake jefowa game da shi, kuma duk da akwai amsar wasu tambayoyi masu yawa a littattafan magabata, sai dai har yanzu akwai dunkulallun mas’aloli ba bayyanannu ba masu yawa da suka rage wadanda amsoshin da suka gabata ba su kasance masu kashe kishirwar wadanda suke da tambaya a wannan zamani ba.

4- Saboda muhimmancin mas’alar imamanci da kuma kasancewarta asasin ginin tunani da aiki na Shi’a, makiya sun yi kokarin jefa shubuhohi game da imam Mahadi (A.S) domin masu imani da shi su samu shakku da kaikawo kan al’amarinsa kamar shubuha a kan asalin haihuwarsa, ko tsawon rayuwarsa, da suke nuna wa kamar wani abu ne da yake mustahili, ko kuma buyansa da fakurwarsa ga barin ganin mutane da suke nuna wani abu ne da ya saba wa hankali da kuma soke-soke da wasu daruruwan shubuhohi da suke kawowa.

Wani lokaci kuwa wasu mutane ba tare da kula ba ko kuma saboda rashin sanin koyarwar Ahlul Baiti (A.S), da kuma kuskuren ko mummunan fahimta maras asasi game da al’amarin mahadiyyanci ba sukan yi kokarin kawo bincike game da hakan, da haka ne wasu sukan kauce ko ma suka kauce wa hanya. Misali game da sauraren zuwan imam Mahadi (A.S) da kuma yake-yakensa da kuma yiwuwar haduwa da shi a lokcin buyansa, da yawa an samu rashin fahimta game da hakan wanda suka kawo abubuwan da ba su yi daidai da ruywayoyin da suka zo game da hakan ba, wadannan bahasosi kuwa abubuwa ne na mahallin bincike wanda dole ne ya kasance ta hanyar ingantaccen bincike na hankali game da bahasin imam Mahadi (A.S).

Bisa haka ne da kuma la’akari da abin da ya hada da tarihin rayuwarsa mai tsarki aka yi kokarin bincike game da amsoshin tambayoyi game da shi kansa imam Mahadi (A.S) a wannan littafin, da kuma abin da yake da alaka da tarihin rayuwarsa, kuma dukkan shubuhohin da ake jefawa game da shi an yi bincikensu an kuma bayar da amsa game da su. Da fatan wannan ya zama wani taku da taki na farko domin kaiwa zuwa ga sani mai zurfi game da hujjan Allah na karshe a bayan kasa, imam Mahadi (A.S).

 [1] - Biharun anwar, j 15, sh 160.

[2] - Haman, j 2, shafi 100.

comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.