Bukatuwa Ga Imami (A.S)

Bukatuwa Ga Imami (A.S)

Related Articles

Game da wajabcin samuwar imami akwai dalilai da dama da aka yi bayanin hakan, amma mu a nan zamu kawo wasu bayanai ne takaitatttu.

Dalilin da yake nuna wajabcin bukatuwa zuwa ga annabi shi ne dalilin da yake tabbatar da bukatar imami, domin musulunci shi ne addinin karshe kuma Muhammad (S.A.W) shi ne karshen annabawan Allah, saboda haka ya zama dole ne musulunci ya amsa dukkan bukatun dan Adam har zuwa alkiyama.

Ta wani bangaren kuma Kur'ani mai girma shi ne asasin dukkan hukunce-hukuncen Allah wanda bayaninsa yake kan wuyan Manzo (S.A.W), amma kuma a fili yake cewa Manzo (S.A.W) a matsayinsa na jagoran al’ummar musulmi ya yi bayanin bukatun da suka kebanta da zamaninsa ne, kuma dole ne a samu wani mai maye gurbinsa domin ya ci gaba da bayani ga al’umma, wanda yake masani da ilimin sakon domin ya yi bayanin abin da Manzo (S.A.W) ya bari na daga bayanai, da kuma amsa bukatun musulmin kowane zamani.

Haka nan imamai (A.S) su ne masu gadin gadon da Manzo (S.A.W) ya zo da shi, masu kuma bayani da fassarar Kur'ani domin kada addinin Allah ya samu karkacewa daga tafarkinsa da hadafinsa a hannun makiya, ya kuma wanzu mai tsarki har zuwa ranar kiyama.

Bayan haka, dole ne imami ya zama mutum kamili, koyi ga al’umma a kowane bangaren rayuwa na dan Adam, domin ya zama misali ga mutum, wanda ta haka ne za a tarbiyyatar da dan Adam zuwa ga kamalarsa, kuma ya zama karkashin tarbiyyar mai tarbiyyar da yake da alaka da Allah madaukaki, kuma ya kare shi daga karkacewa da fadawa hannun shaidan na zahiri.

Daga abin da muka fada a sama ne zamu fahimci cewa bukatarmu zuwa ga imami bukata ce ta rayuwa, kuma zamu kawo wasu daga ayyukan imamai (A.S);

1. Jagoranci da tafiyar da al’amuran al’umma (kafa hukuma).

2. Kare addinin da Manzon rahama ya zo da shi daga Ubangiji daga karkacewa da kuma bayanin Kur'ani bayani ingantacce.

Tsarkake rai da shiryar da mutane zuwa ga kyawawan dabi’u.

comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.