Siffofin Hukumar Imam Mahadi (A.S)

Siffofin Hukumar Imam Mahadi (A.S)

Related Articles

Fagen Wannan Hukuma Ta Imam (A.S)

Ba kokwanto cewa; hukumar imam Mahadi (A.S) hukumar duniya ce, saboda dukkan burin dan Adam yana cikinta. Don haka zamu yi nuni da wasu ruwayoyi da suke bayani game da hakan:

A-Ruwayoyin da suke nuna imam Mahadi (A.S) zai cika bayan kasa da adalci[1], kalmar bayan kasa a nan ta game dukkan duniya ne, kuma babu wanni dalili da yake nuna wani bangare na duniya ake nufi.

B-Ruwayoyi da suke nuna salladuwar imam Mahadi (A.S) a dukkan duniya, kuma wasu garuruwan ma sun zo a wasu ruwayoyi a matsayin misali ne.

a wasu ruwayoyin an yi magana game da Rum, Chaina, Dailam ko kuma duwatsun Dailam, Turkawa, Sind, Hind, Kisdandiniyya, Kabul shah, da Khazar, a matsayin wasu yankuna da imam Mahadi (A.S) zai mamaye su, kuma ya bude su[2].

Kuma sananne ne cewa wadannan yankuna a lokacin ruwaya suna da fadi mai yawan gaske, misali; Rum a lokacin ta hada dukkan turai ne har yankin Amurka, Chaina kuma ta hada dukkan Asia ta gabas ne, wanda ya hada Japan, Hind kuma ta hada har da Pakistan.

Birnin Kisdandiniyya kuwa cin nasara kansa wata nasara ce mai girma da take nuna nasarar saukake shiga turai ta gabas cikin sauki.

A takaice salladuwar imam Mahadi (A.S) kan yankuna masu muhimmanci yana nuna fadadar daular duniya ne ta imam Mahadi (A.S).

C-Wasu ruwayoyin da suke nuna fadadar daular imam Mahadi (A.S) duk duniya.

Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: Addinina zai yi nasara tahannun a kan dukkan addinai… kuma da juyin imam Mahadi (A.S) dukkan duniya za a tsarkake ta daga makiyana, kuma zai yi shugabanci gabas da yammacin duniya gaba daya[3].

Imam Muhammad Bakir (A.S) yana cewa: mai juyi daga cikinmu… mulkinsa zai kai gabas da yamma, kuma Allah mai girma da daukaka zai dora addinsa a kan addini dukkaninsa koda kuwa mushirikai sun ki…[4]

Amma hedkwatar daular imam Mahadi (A.S) kamar yadda ya zo a tarihi ita ce birnin Kufa, kuma a wancan zamanin ta hada har da Najaf, don haka ne ma wasu ruwayoyi suke nuna Kufa wasu kuma sukan zo da ambaton Najaf.

A wata ruwaya imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa: cibiyar hukmarsa (imam Mahadi) ita ce birnin Kufa, Kuma masallacinta ne wajen hukuncinsa[5].

Mun sani cewa Kufa ita ce hedkwatar daular imam Ali (A.S) kuma a masallacinta wanda yake daya daga mash'huran masallatai hudu na duniya yake salla kuma yake yin huduba, kuma a nan ne ya yi shahada.

 

Muddar Hukumar Imam Mahadi (A.S)

Duk da cewa hukuncin zalunci ya tsawaita, amma zai kawu da bayyanar hujjar Allah a bayan kasa imam Mahadi (A.S), Kuma hukumarsa zata cigaba har sai kwanankin duniya sun kare, kuma zalunci har abada ba zai maimaitu ba, don haka daular Ahlul Baiti (A.S) zata kasance daular karshe a duniya.

Manzon rahama (S.A.W) yana fada cewa: bayan hukumar imam Mahadi (A.S) daularsa zata cigaba da wanzuwa har zuwa tashin kiyama, kuma jagorancin duniya zai ci gaba a hannun mabiyansa masoyansa hannu da hannu[6].

Imam Muhammad Bakir (A.S) ya ce: daularmu ita ce karshen dauloli, kuma babu wasu al'umma sai sun yi daula kafin daularmu, domin kada lokacin da zamu yi tamu hukumar wani ya ce: mu ma da mun samu yin hukuma da mun yi irin hakan[7].

Don haka tsawon daular imam Mahadi (A.S) ya wuce tsawon muddar shi kansa imam Mahadi (A.S) da rayuwarsa (A.S), domin shi mai rasuwa ne kuma ya bar daular a hannun masoyansa.

Ba mamaki cewa imam Mahadi (A.S) zai iya kawo canji a duniya gaba daya, amma tsawon shekaru nawa zai dauka wannan wani abu ne wanda ba mai iya hasashensa, don haka dole ne a koma zuwa ga ruwayoyi masu bayani game da hakan.

Koda yake idan mun yi la'akari da siffofin imam Mahadi da mataimakansa da da kuma tsarin da yake hannunsa wannan al'amari ne wanda zai iya wakana cikin shekaru kadan kasa da goma.

Ruwayoyin da suke yi magana game da tsawon hukumar imam Mahadi (A.S) sun zo da sabani kamar 5, wasu kuma 7, wasu 8, wasu 9 da 10. wasu kuma sun zo da 19 da watanni, wasu 40, wasu 309[8].

Sakamakon sabanin da yake cike dawadananruwayoyi sanin hakikanin tsawon daularsa abu ne mai wahla, amma abin da ya shahara a gun malamai shi ne: shekaru 7[9].

 Wasu ruwayoyi sun zo da cewa daular imam Mahadi shekaru 7 ne kowace shekara tana datsawon shekaru goma irin namu:

Wani ya tambayi imam Ja'afar Sadik (A.S) game da tsawon daular imam Mahadi (A.S) sai ya amsa masa da cewa: shekaru bakwai ne, kuma kowace shekara tana da tsawon shekaru saba'in daga shekarunku na yau[10].

Majlisi yana cewa: ruwayoyi masu yawa sun zo game da tsawon hukumar imam Mahadi (A.S) amma dole ne mu fassara su da cewa: wasu sun zo game da tsayin muddar hukumarsa, wasu kuma da shekarun muddar tabbatar hukumarsa, wasu kuma tana magana da ranaku ne da muka san su, wasu kuma suna magana ne kan ranaku da watanni da suke a zamanin da zai zo, amma Allah shi ne ya fi kowa sani[11].

 

Dabi'ar Hukumar Imam Mahadi (A.S)

Kowane shugaba yana da hanyar da yake tafiyar da daularsa, imam Mahadi (A.S) ma yana da tasa hanyar tafiyar da al'amuran daula, kuma duk da cewa mun yi nuni da yadda hukumarsa take a baya, amma saboda muhimmancin wannan maudu'I zamu yi nuni zuwa gareshi daga maganganun Manzon rahama da imamai (A.S).

A cikin ruwayoyi an yi bayani ne game da

Dabi'arsa da halayyarsa ta tafiyar da daularsa a dunkule ne, da nuni da cewa tafarkinsa irin na manzon Allah ne (S.A.W), wanda yake shi ne mai lamunci rayuwa mai kyau a duniya da lahira.

Imam Ja'afar Sadik yana nuni da wannan yana mai cewa: zai yi kamar yadda manzon Allah (S.A.W) ya yi, ya rushe abin da ya gabace shi kamar yadda Manzo ya rusa al'amarin jahiliyya, sai ya kafa musulunci sabo (tun daga farko)[12].

Koda yake akwai wasu canje canje sakamakon yanayi da zamu yi magana game da su a wasu ruwayoyin daban.

 

 

Tafarkinsa Na Jihadi Da Yaki

Imam Mahadi (A.S) zai hana yaduwar shirka da kafirci a duniya, kuma zai yi kira zuwa addinin musulunci ne.

Game da rayuwarsa ta jagoranci da tafiyar da al'amuran al'umma Manzon rahama (S.A.W) yana cewa: Tafarkinsa (hanyar gudanarwarsa) irin nawa ne, kuma zai tabbatar da mutane kan addini da shari'a[13].

Imam Mahadi (A.S) zai bayyana ne a lokacin da gaskiya zata bayyana ga kowa kuma hujja ta hau kan kowa ne.

Ya zo cewa: imam Mahadi (A.S) zai futo da Attaura da Injila da ba a canza su ba a Andakiya, kuma da wannan ne zai kafa wa Yahudawa da Kiristoci hujja, kuma mafi yawansu zasu musulunta[14].

A wannan lokacin fikirar musulunci zata yadu cikin addinai daban-daban, kuma da taimakon Allah ga imam Mahadi (A.S) da kuma alamomi da yake tare da su kamar sandar annabi Musa (A.S) da zoben annabi Sulaiman (A.S), da takobi da tutar manzon Allah[15] (S.A.W) domin kafa adalci a duniya gaba daya.

A fili yake cewa bayyana wa duniya irin wadannan alamomi zai sanya ta fuskantar gaskiya, wadanda zasu rage kan hanyar bata zasu kasance mutane ne wadanda suke rasa mutumtakarsu. Kuma mu sani takobin imam Mahadi (A.S) ba zata bar wani mai fasadi a bayan kasa ba, wannan kuwa tafarki ne na Manzon rahama (S.A.W)[16].

 

Halayyarsa Ta Kotunsa (Hukuncinsa)

A wannan bangare imam Mahadi (A.S) zai yi aiki da tafarkin kakansa imam Ali (A.S) ne, kuma zai bi hakkin da aka take ya kwace shi da karfi, kuma ya mayar da shi ga ma'abotansa.

Wannan shi ne adalcin da mutane suke neman gani a yau, kuma da wannan tafarkin nasa ne zasu samu amfanuwa daga adalcinsa[17].

Wasu ruwayoyi sun zo da bayanin cewa imam Mahadi (A.S) zai yi hukunci kamar irin na Dawud da Sulaiman (A.S) ne, kamar yadda suke hukunci da ilimin Allah, ba tare da neman shedu ko rantsuwa ba.

Imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa: yayin da imam Mahadi (A.S) zai bayyana zai yi hukunci irin na Dawud da Sulaiman (A.S), ba zai karbi sheda ba[18].

Tayiwu sakamakon dogaronsa da ilimin Allah ne zai iya tabbatar da adalci na hakika, amma da ya dogara da shedu to abin da za a iya samu ita ce adalci na zahiri, wanda yake akwai tsammanin yin kuskure matuka a ciki.

Koda yake wannan hanya tana da wahalar gaske, amma za a iya fahimtar cewa wannan hanyar hukunci ta yi daidai da zamaninsa (A.S).

 

Halayyarsa Ta Tafiyar Da Al'amuransa

Idan aka samu ma'aikata masu dacewa na gari, to aikin kasa da isa zuwa ga hadafinta yakan yi sauki sosai. Imam Mahadi (A.S) a matsayinsa na shugaban hukumar duniya zai zaba wa kowane yanki na duniya mutumin da ya dace da shi, kuma su mutane ne wadanda suka cancanta ta kowace fuska kamar tafiyar da al'amura, ilimi, tsarki, niyya da aiki, da jarumtaka wajen daukar mataki.

Imam Mahadi (A.S) a matsayinsa na mai yanke hukunci a hannunsa shi ne wanda tafiayr da al'amuran kasa yake gudana karkashin kulawarsa. Kuma yana bincike kan ma'aikatansa bincike mai tsanani.

Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: alamar imam Mahadi (A.S) shi mai tsanani ne kan ma'aikata, mai kyauta ne da dukiya, mai tausayi ga miskinai[19].

 

Halayyarsa Ta Tattalin Arziki

Tsarin imam Mahadi (A.S) kan dukiya shi ne a raba ta da daidaito, kuma wannan shi ne tsarin da ya gudana a lokacin Manzon rahama (S.A.W), sai dai abin takaici da bakin ciki an samu wasu mutane da suka canja tsarin da Manzon rahama ya zo da shi, sai wannan ya haifar da bambancin dabakoki a cikin al'ummar musulmi, har wasu daga cikin al'umma suka mayar da dukiyar kasa kamar ta kashin kansu, kuma suka rika yin amfani da ita don maslaharsu, kuma wannan al'amri ya kasance sakamakon kafa hukumominsu da ba na shari'a ba, dukiya ta kasance na dangin halifa, har ma an samu daga halifofi wanda ya kebance dukiya ga bani Umayya.

Imam Mahadi (A.S) wanda yake shi ne alamin bayyanar adalci da hukuncin gaskiya, zai sanya Baitul mali a matsayin dukiyar tarayya ta al'umma gaba daya, ta yadda babu wani nau'in kebancewa ga dukiya da zai sake wakana.

Manzon Allah sawa yana cewa: idan imam mai juyi (Mahadi) daga cikinmu ya zo, zai kawar da shinge da hurumi (wato wasu yankuna ne da sarakuna suke kebance wa kawukansu) ta yadda babu wani shinge da zai rage[20].

Kuma dukiya a lokacin zata kasance domin biyan bukatun mabukata ne da kawar da talauci, imam Mahadi (A.S) yana ba wa mutane dukiya mai yawa ne kuma duk wanda ya bukaci wani abu wajensa yana ba shi dukiya mai yawa ne.

Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: yana bayar da dukiya da yawa[21].

Wannan kuwa ita ce hanyar da za a samar da gyara a cikin al'umma, da cimma hadafi mafi girma, da kawar da talaucin al'umma, da samar da yanayi da zai sanya mutane fuskantar Allah da bauta masa.

 

Halayyar Imam Mahadi (A.S)

Game da halayyarsa da mutane shi yana matsayin shugaba ne kuma jagora mai alaka da mutane da yake ganin hukuma a matsayin wata wasida ta yin hidima ga mutane ne, da kuma kaiwa ga kololuwar kamala, da kuma katse hannayen azzalumai daga bautar da bayin Allah.

A bisa hakika shi yana da tafarki irin na imam Ali (A.S) ne wanda yake da dukiyar al'umma a hannunsa amma shi yana rayuwar talauci ta kasa ta karshe.

Game da shi imam Ali (A.S) yana cewa: imam Mahadi s zai dauka wa kansa alkawarin zai yi rayuwa kamar na mutanensa kuma ya sanya abin da suke sawa, ya hau abin da suke hawa… ya wadatu da kadan[22].

Imam Ali (A.S) shi kansa ya yi irin wannan rayuwa ne a duniya a abinci da tufafi, kuma ya yi koyi da manzon Allah (S.A.W) ne, kamar yadda imam Mahadi (A.S) zai yi koyi da su.

Imam Ja'afar Sadik (A.S) yana cewa:

Idan mai juyinmu (Imam Mahadi) ya zo, zai ya sanya tufafi irin na Ali, kuma ya tafiyar da al'umma da irin hanyarsa[23].

A daidai lokacin da yake tsanantawa kansa rayuwa, sai gashi kuma ga al'umma ya kasance kamar uba ne mai yawan tausayi ga 'ya'yansa, kuma a kodayaushe yana neman abin da zai kawo musu sauki ne, ta yadda imam Rida (A.S) a wata ruwaya yake siffanta shi yana mai cewa: imami ne mai tausasawa da jinkai, kuma uba mai tausayawa, kuma dan'uwan mai tausayawa, kuma uwa mai kyautatawa ga danta karami, mai gaggauta bayar da mafaka ga al'umma a cikin musiba mai ban tsoro[24].

Daga manzon Allah (S.A.W) game da imam Mahadi (A.S) yana cewa: shi ne al'ummarsa take fakewa gunsa, kamar yadda kudan zuwa suke fakewa gun sarauniyarsu[25].

 

Yardar Mutane

Daya daga abubuwan da suke jan hankalin mutane game da hukumomi shi ne yardar mutane. Amma daular imam Mahadi (A.S) zata samu karbuwa da yardar mutane gaba daya, ba kawai mutanen duniya ba, har ma mutanen sama zasu yarda da wannan hukuma ta adalci.

Manzon rahama (S.A.W) yana cewa: ina yi muku albishir da imam Mahadi (A.S) da mutanen sama da kasa zasu yarda da hukumarsa. Yaya kuwa wani ba zai yarda da hukumar imam Mahadi (A.S) ba, alhalin dukkan duniya ya haskaka da bayyana gareta cewa; gyaran al'amarin dan Adam na duniya da lahira yana iya wakana ne kawai a hukumar Allah madaukaki[26].

Muna iya cika wannan maganar da wani bangare na maganar imam Ali (A.S) domin kyautata kammalawa da yake cewa: …Ubangiji zai karfafe shi da mala'iku, kuma ya kare mataimakansa, kuma ya taimaka masa ta hanyar alamominsa, kuma ya sanya shi mai galaba a kan mutanen duniya, kuma ya sanya su masu zuwa gareshi jama'a-jama'a suna masu son ransu da kuma bisa tilas, kuma zai cika duniya da adalci da haske da dalili. Kasashe zasu yi imani da shi har sai ya kasance babu wani kafiri da zai rage sai ya yi imani, kuma munanan ayyuka ba zasu rage ba sai sun koma kyawawa, kuma a hukumarsa masu fika (dabbobin daji masu kisan namun daji) zasu yi sulhu tsakaninsu, kuma duniya zata fito da dukkan albarka, kuma sama ta kwararo alheranta, kuma taskokin duniya zasu bayyana gareshi… to farin ciki ya tabbata ga wanda ya ga wannan rana, ya ji maganarsa[27].

 

 


[1] Kamaluddini: babi 25, h 4, Da kuma: babi 24, h 1 da 7.

[2] Gaiba, nu'umani da kuma: ihtijaj na dabrasi.

[3] Kamaluddini, j 1, babi 23, h 4, shafi: 477.

[4] Kamaluddini, j 1, babi 32, h 16, shafi: 603.

[5] Baharul anwar, j 53, shafi: 11.

[6] Kamaluddin, j 1, babi 23, h 4, shafi: 477.

[7] Gaiba, Dusi, fasali 8, h 493, shafi: 472.

[8] Najmuddin, dabasi, shafi: 173 – 175.

[9] Al'Mahadi, sadaruddin sadar, shafi: 239.

[10] Gaiba, nu'uman, fasali 7, h 497, shafi: 474.

[11] Biharul anwar, j 52, shafi: 280.

[12] Gaiba, nu'umani, babi 13, h 13, shafi: 236.

[13] Kamaluddin, j 2, babi 39, h 6, shafi: 122.

[14] Alfitan, shafi: 249 – 251.

[15] Isbatul hudat, j 3, shafi: 439 – 494.

[16] Abin da ya gabata, shafi: 450

[17] Alfitan, shafi: 99.

[18] Isbatul huda, j 3, shafi: 447.

[19] Mu'ujamu ahadisil Mahadi (A.S), j 1, shafi: 246, h 152.

[20] Biharul anwar, j 52, shafi: 309.

[21] Mu'ujamu ahadisil Mahadi (A.S), j 1, shafi: 232, h 143.

[22] Muntakhabul asar, fasali 6, babi 11, h 4, shafi: 581.

[23] Wasa'ilus Shi'a, j 3, shafi: 348.

[24] Usuluul kafi, j 1, h 1, shafi: 225.

[25] Muntakhabul asar, fasali 7, babi 7, h 2, shafi: 598.

[26] Biharul anwar, j 51, shafi: 81.

[27] Isbatul hudat, j 3, shafi: 524.

comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.