Kuskuren Fahimta

Kuskuren Fahimta

Related Articles

 

1-kuskuren fahimtar ma'anar sauraro, ya sanya wasu suna tsammanin cewa: tun da gyara da kawar da fasadi zai kasance a hannun imam Mahadi (A.S) ne, to ba su da wani nauyi da ya hau kansu na gyara da kawar da fasadi a cikin al'ummarsu. Wasu ma suna ganin cewa dole ne su yada fasadi a bayan kasa domin imam Mahadi (A.S) ya bayyana! Irin wadannan miyagun tunanuka sun saba wa koyarwar Kur'ani da Ahlul Baiti (A.S) na umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna da suka dora su a wuyan dukkan musulmi gaba daya.

Imam khomaini jagoran juyin musuluncin Iran yana cewa: idan dai hannunmu zai iya kaiwa to hukuncin shari'a ya hau kanmu na wajabcin mu tafi ko'ina mu kawar da dukkan zaluncin da yake duniya, sai dai mu ba zamu iya ba. Amma kasancewar wannan aiki ne da imam Mahadi (A.S) zai yi shi a duk fadin duniya, ba yana nufin ku kawar da hannunku daga (yakar zalunci ba) na aikin da ya hau kanku na (umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna), wannan ba yana nufin ba ku da wani takalifi a kanku ba[1].

Ya ci gaba da cewa: shin mu zamu yi aiki ne sabanin Kur'ani ne mu bar hani ga mummuna da umarni da kyakkyawa domin kawai tunanin cewa imam Mahadi (A.S) zai zo[2]?!

Don haka ya zama dole mu yi bincike game da sahihiyar ma'anar sauraro.

2-Wasu ruwayoyi suna nuni da cewa duk wani motsi na gyara kafin bayyanar imam Mahadi (A.S) to abin mayarwa ne, don haka motsi da samar da juyi domin yakar dagutu wani abu ne mummuna kamar wanda ya faru a juyin musuluncin Iran.

Amma muna iya amsa wannan da cewa; gudanar da dokokin Allah wani abu ne wanda yake wajibi, amma ba zai iya samuwa ba sai da tsayar da hukuma mai adalci da zata tsayar da hukuncin Allah.

Na biyu wadansu ruwayoyin sun yi nuni da cewa: abin nufi irin wadannan motsi da babu hasken shari'a a cikinsu ko kuma wadanda ake yi ba tare da sharudda sun cika ba.

Kuma ana iya fassara wannan da irin kiraye kiraye da masu yinsu suke da'awar mahadiyyanci[3].

3-Daya daga mummunar fahimta game da imam Mahadi (A.S) shi ne nuna shi kamar wani mutum mai yawan fushi da aiki da karfin tuwo:

Sabanin yadda mutane da yawa suka dauka ne cewa; imam Mahadi (A.S) zai zo da takobin adalci ne mai yawan zubar da jini kamar tafkuna, amma duba zuwa ga abin da ya zo a ruwayoyi; imam Mahadi (A.S) shi ne hakikanin tausayi da rahamar Allah madaukaki, kuma shi ma kamar yadda Manzon rahama ya yi ne na kira da dalilai bayyanannu da kuma kiran mutane zuwa ga Kur'ani, don haka babu wani wanda zasu yi taho mu gama da shi sai masu gaba da Allah madaukaki.

 

 

[1] Sahifeye nur, j 20, shafi: 196.

[2] Sahifeye nur, j 20, shafi: 196.

[3] Dod gustare jehan, shafi: 254 – 300.


comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.