Imam Mahadi Adon Halitta

Imam Mahadi Adon Halitta

Related Articles

Babban hadarin da duniyar dan Adam take fuskanta shi ne; a kodayaushe muka karanta hadisi mai cewa: “Wanda ya mutu bai san imaminsa (jagoransa) ba, ya yi mutuwar jahiliyya”[1]. Amma saudayawa mutane sukan karanta su wuce ba tare da wani gezau ba, ko tunani mai zurfi da zai sanya su komawa cikin binciken al’amarin wannan imami (A.S) da ya shafi makomarsu da lahirarsu ba.

Da dan Adam ya san hakikanin rayuwarsa da abin da ya hau kansa da makomarsa da karshen rayuwarsa ta duniya, da ya kasance mutum mai kamalar gaske, da mafarkin da yake yi game da aljannar duniya ya tabbata, sai dai son rai da ya yi yawa a zukata, da son holewa da rashin jin sauke nauyin da ya hau kan dan Adam ya sanya shi gafala daga abin da yake shi ne ainihin hadafinsa na duniya da lahira. Kuma duk wani addini ko mazhaba da ya iya samar wa dan Adam hakikanin makomarsa a karshen duniya to hakika shi ne addini ko mazhabin da yake na gaskiya, kuma dole ne sauran su sallama masa su mika wuya.

Wannan littafin da Muhammad Mahadi Ha’iri Fuur, Da Mahadi Yusufiyan, Da kuma Muhammad Amin Bolo Dastyan suka rubuta da yaren Farisanci, ni kuma na fassara shi daga Farisanci zuwa Hausa, littafi ne mai muhimmanci matukar gaske. Lallai littafi ne da tabbas yana daya daga mafi girman abin da zai iya kawar da kishirwar da take cikin al’ummar duniya da ya shafi dukkan wani dan Adam mai tunani a bayan kasa, ba tare da la’akari da addininsa ko mazhabarsa ba.

Kalmar tauhidi tana kunshe cikin sanin imamin zamani, domin idan ba a san shi ba, kuma ba a yi aiki da abin da ya yi umarni ba, babu wani aiki da Allah zai karba daga mai sabawa, don haka ne ma hadisi madaukaki da aka ambata a sama ya yi nuni da cewa; mai irin wannan hali mutuwarsa daidai take da mutuwar ‘ya’yan jahiliyya. Don haka ne yana kanmu mu yi tunani domin sauke nauyin da ya hau kanmu na sanin imamin zamaninmu da kuma yin aiki bisa tafarkinsa.

Ga Allah muke neman dacewar duniya da lahira, kuma babu karfi ko dubara sai gareshi. Allah ya sanya mu cikin wadanda yake yi wa rahama da gafararsa domin imamin wannan zamani, imam Mahadi dan Hasan Askari (A.S).

Hafiz Muhammad Sa'id Kano Nigeria, hfazah@yahoo.com

13 Rabi’ul awwal 1427, 23 Parbardin 1385, 12 Afrilu 2006

 

 

[1] Sharhu ihkakul hakk, Sayyid mar’ashi najafi, j 13, s: 86.

 


comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.