Ana sayar da 'yan Najeriya kamar awaki — Buhari

Ana sayar da 'yan Najeriya kamar awaki — Buhari

Buhari ya bayyana haka ne ranar Talata da daddare a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast.

Shugaban na Najeriya, wanda ke yin jawabi ga 'yan Najeriya mazauna kasashen waje, ya sha alwashin rage yawan 'yan kasar da ke yin ruguguwa wajen zuwa Turai.

Buhari na magana a daidai lokacin da rahotanni suka nuna yadda ake sayar da bakaken fata - cikinsu har da 'yan Najeriya a kasar Libya - a matsayin bayi a kan kudin da bai wuce $400 ba (N144,000).

"Abin takaici ne yadda ake sayar da 'yan Najeriya a matsayin bayi tamkar wasu awaki a kan daloli kalilan", in ji Shugaba Buhar

Lamarin da ya ya tayar da hankulan sassa daban-daban na duniya, musamman nahiyar Afirka.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce za a koma da dukkan 'yan Najeriya 'yan ci-rani da suka makale a Libya gida.

Shugaban ya musanta yawan 'yan Najeriyar da aka ba da rahoton mutuwarsu a lokacin da suke bi ta Bahar Rum domin zuwa Turai a kwanakin bayan.

"An ce 'yan Najeriya 26 ne suka mutu a Bahar Rum; amma an binne su ba tare da an tantance su ba.

"Sai dai shaidun da mai ba ni shawara kan harkokin kasashe waje Mrs. Abike Dabiri-Erewa ta kawo min su nuna cewa mutum uku ne kawai 'yan Najeriya," in ji shugaba Buhari.

Hukumar kaura ta duniya dai ta ce ko da a ranar Talata sai da aka koma da 'yan Najeriya 140 gida daga Libya, cikin wadanda suka makale a can.

comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.