Imam Askari

Imam Askari

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Imam Hasan Askari (a.s)
Imami Na Sha Daya: Imam Hasan Askari Dan Ali Al-Hadi (a.s)
Sunansa da Nasabarsa: Alhasan dan Ali dan Muhammad dan Ali (a.s). Babarsa; kuyanga ce mai suna Susan. Al-kunyarsa: Abu Muhammad. Lakabinsa: Al-askari, Assiraj, Al-khalis, Assamit, Attakiyyi. Tarihin haihuwarsa: 8 Rabi'ul Awwal 232H. Inda aka haife shi: Madina.
Matansa: Kuyanga ce ana cewa da ita Narjis. 'Ya'yansa; Daya ne shi ne Imam Mahadi Al-muntazar. Tambarin zobensa: Subhana manlahu makalidus-Samawati wal Ardi.
Tsawon rayuwarsa: Shekara 28H. Tsawon Imamancinsa: Shekara shida. Sarakunan lokacinsa: Al-mutawakkil da Al-mustansir da Al-musta'in da Al-mu'utaz da Al-muhtadi da Al-mu'utamad. Tarihin shahadarsa: 8 Rabi'ul Awwal 260 H.
Inda ya yi shahada: Samra'u. Dalilin shahadarsa; An kashe shi da guba a lokacin Al-mu'utamad. Inda aka binne shi: a gidansa na Samra'u a Irak.
Shi ne Hasan Askari dan Ali (A.S) kuma babarsa Hudais (A.S), an haife shi a Madina ranar juma'a takwas ga watan Rabi'ul awwal an ce litinin goma ga Rabi'ul awwal , shekara ta dari biyu da talatin da biyu hijira, kuma ya yi shahada da guba a ranar juma'a bakwai ga watan Rabi'ul awwal shekara ta dari biyu da sittin hijira, kuma dansa Imam Mahadi (A.S) shi ne ya shirya janazarsa, kuma ya binne shi gun kabarin babansa Imam Hadi (A.S) a Samarra inda ake ziyartarsa a yau.
Ya kasance misali a falala da ilimi da daukaka da jagoranci da ibada da kaskan da kai, kuma ya kasance mai kyawun jiki da fuska, madaidaicin jiki, kuma yana da soyayya mai yawa a zukatan mutane, da matsayi a cikin rayuka, ya kasance yana kama da kakansa Manzon Allah a dabi'unsa da kyawun dabi'arsa da kuma kyakkyawan zamansa tare da mutane.
Daga cikin kissoshin karamarsa abin da Isma'il ya ruwaito yana cewa: na zauna masa a kan hanya sai ya wuce ni sai na kai kukan talauci gunsa, sai ya ce: ka rantse da Allah kana mai karya alhalin ka binne dinare dari biyu, amma ba na fada maka hakan ba ne domin in hana ka, ba shi abin da yake gun ka ya kai yaro, sai yaronsa ya ba ni dinare dari .
Wani mutum ya fuskance shi yayin da ya ji labarin kyautarsa yana mai bukatar dirahmi dari biyar, sai Imam (A.S) ya ba shi dirhami dari biyar da kuma wasu dari uku daban .
Kuma kowa ya yi masa shaida da baiwa da daukaka har da kiristoci sun yi shaida da cewa yana kama da Isa masihu (A.S) a falalarsa da iliminsa da kyautarsa da mu'ujizarsa, ya kasance mai yawan idaba, mai yawan tahajjudi, mai yawan gyara da kuma kwarjini.

comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.