Matsayin Sayyida Fatima

Matsayin Sayyida Fatima

Related Articles

Mai karatu a yau muna tafe ne da jawabin Maulidin Sayyida Fatimatuz Zahra (AS) na ranar farko da yammacin ranar Juma’a 18 ga Jimada Sani,1435 (18/4/2014) a Husainiyya Bakiyyatullah, Zariya. Ammar Muhammad Rajab ne ya rubuto mana. A sha karatu lafiya.
Assalamu alaikum warahmatullahi Ta’ala wabarakatuhu.
To, zan fara da taya mu murnar zagayowar haihuwar Sayyidatun Nisa’il alamin. Wadannan kwanukan, insha Allah, muka dauka kwanakin bukukuwa na tunawa da ranar haihuwarta. Ranar haihuwarta takamaime ashirin ne ga watan Jimada Ath-thaniya. Amma kusan ma tun makon da ya wuce, kusan a wurare ana ta bukukuwa daban-daban na tuna ‘wiladarta.’ Muna iya cewa; tun dai bayan uku ga wata, wanda aka tuna shahadarta, har ya zuwa yanzu, kusan ana ta tuna haihuwa din. Hususan mu anan, wanda yake mun samu kanmu a wani bangare na duniyar musulmi, wanda ya jahilci ita Sayyadatu Nisa’il alamin.
Ga shi a rubuce, inda za ka tambayi kowane musulmin da ya yi karatu, wace ce Shugabar mata gaba daya? Zai ce maka Fatima ce! Duk da ma akwai ma yunkuri da aka yi tun a farko, lokacin mulkin Banu Umayya na cire wannan din. Da cewa; kamar misali, akwai yunkurin na nuna cewa; a’a Sayyada Maryam ita ce Sayyidati Nisa’il alamin. Saboda Allah (T) ya ce “wasdafaki ala nisa’il alamin.” Kuma ya saukar da sura sukutum dangane da ita. Har ma suna cewa; ina suratu Fatima? Amma akwai surar Maryam. Amma dai ya tabbata a ingantattun hadisai wadanda duk suka ruwaito cewa; ita ce Shugaba a duk mata.
Na’am akwai wasu mata da suka samu manyan matsayi. Daga cikin su akwai; Maryam ’yar Imran (SA) da kuma Khadija bnt Kuwalid, Mahaifiyar Sayyida Fatima (SA) da kuma Asiya bnt Muzahim, akan ce ma ta matar Fir’auna, wanda Fir’aunan ne ya kashe ta. Wanda Allah (T) ya ba da misali da ita da Maryam a cikin misaloli. Wato ga ta bangare guda, idan ka tambayi mutane a karatu, za su ce maka sun karanta. Amma me suka sani dangane da Sayyida Fatimatuz Zahra? Abin da suka sani kadan ne.
To, kuma na yi wata magana a lokacin Shahadarta (Sayyida Zahra din), na yi wani dan ‘mukaddima,’ wanda ba laifi in dan tabo mana kadan. Na cewa; idan mutum yana da daraja, to, lazim ne ya zama an ga, ko kuma an san wani abu da ya ‘ahhala’ shi da wannan daraja din. In ba haka ba zai zama rayawa kawai, mujarradin rayawa. Alal misali, da za a yabi wani mutum, a ce masa shahararren mawaki ne, ‘masalan,’ to, lallai mutane za su so su ji wakensa. Idan suka shafa suka ji ai ko baiti daya na wake ma bai taba rairawa ba, sai a ce to, ya aka yi ya zama shahararren mawaki?
Da za a ce mutum ai jarumi ne, mayaki, za su so su ji fagagen da ya kwakkwama. Idan aka shafa, ashe ma bai taba kwamawa ba, to, ta ina ya zama jarumi? Idan aka ce wannan shahararren dan dambe ne, to, dole a ji su waye ya mammangare? To, sai aka ji kawai ma ko ya sha mangara, ko kuma bai taba damben ba. To, ta ina ne ya zama shahararren dan dambe? Kazalika kuma, idan ka ji ana yabon mutum da wata dabi’a, lallai idan ka shafa za ka ga haka nan. Daga cikin ruwayoyin, misali, kamar inda Allah (T) ya fadi dangane da Annabi Ayyub, Allah (T) ya yaba ma Annabi Ayyub (AS), yana cewa “mun same shi mai dauriya” To, dole ya zama ya daure a kan mene? Idan ka duba, zaka ga, kai, lallai ba karamin dauriya Ayyub ya yi ba, har Allah (T) ya ce masa “Sabir”. In ka ji tarihin irin jarabawar da aka yi ma Annabi Ayyub da kuma har ya kai ga wannan, za ka ga cewa; lallai wannan an makala masa daraja ne domin ya cancanci wannan abin.
Haka kuma, idan ka ji Allah (T) ya ce ma Ibrahim “inna Ibrahima kana ummatan”. Ya siffanta shi da ‘Umma’, ya ce masa ‘Kanit’, ya ce masa ‘Hanif’, ya ce masa ‘Halim’, ya ce masa ‘Khalil’, duk Allah (T) ya ambaci Ibrahima da wadannan siffofin. ‘Halim’, ‘Awwab’, ‘Munib ’ (‘Halimun’, ‘Awwabun’, ‘Munib). ‘Khalil’, ‘Umma’ ‘Kanit’, “walam yakun minal mushrikin”. Siffofi ne da Allah (T) ya siffanta Ibrahim. In ka karanta tarihin Ibrahim, za ka ga, kai, wadannan lambobin girma da Allah (T) ya mammanna ma Ibrahim, lallai bisa cancanta ne, ba haka kawai ne ya siffanta shi da wadannan siffofi ba.
To, idan muka zo, sai mu ga akwai wasu shekarun da aka yi yayin rubuta ‘fada’il’. Da aka zo, wadansu mutane suna da falaloli, kuma ba a son falalolin nasu, sai aka yi kokari aka rufe falalolin. Sai aka dinga kirkiro hadisai ana ta ba mutane ‘fada’il’. To, don kar a ce me ya ‘ahhala’ shi da ‘fadila’ din? To, kuma sai aka shiga wani yayi. Don wannan wani zamani ne. Zamanin mulkin Banu Umayyah. Akwai wani daidai wani lokacin da aka yi haka nan. Ana cewa; shekarar da aka yi ta kirkire-kirkiren ‘tafdil’. Sai a ce; Annabi ya ce kaza dangane da wane. Annabi ma ya ce kaza dangane da wane. Annabi ya ce kaza dangane da wance. Annabi ya ce kaza. Sai ana ta fadar irin wannan. Amma idan mutum ya shafa, hatta a tarihinsu, sai ya zama me ya ‘ahhala’ wannan mutum ga wadannan darajojin da suka ba shi?
To, don haka ma, ka san mutumin da yake karya, sai ya yi ta wani lokaci yadda za ka iya gane shi. Alal misali; da ake kokarin a nuna su masu yawan ibada ne; wani sai aka ce; ainihin ‘kulli yaumin’ ma da Alkur’ani kacokaf ma yake ‘wutiri’. Wanda yake wannan irin daraja, sai mu ce ko Annabi ma bai same shi ba, in dai daraja ne. Amma kuma ma ya saba ma hankali. Wato shi zai yi raka’o’insa na tahajjud. Wanda ‘adatan’ an saba raka’o’in tahajjud akan yi su guda takwas ne. Hudu dogaye, hudu matsakaita. Sannan a yi ‘shafa’i’ da ‘wutri’, sannan a yi ‘raka’atil fajri’, sannan a yi subahi. To, shi wannan gwarzon, sai ya yi dogayen ‘raka’o’in Tahajjud’ da matsakaita. Ya yi gajeren ‘shafa’i’ (ban san ko dogayen ‘shafa’i’ yake yi ba), tunda shi ya bambanta da kowa. To, in ya zo ‘wutri’ maka Malam, sai ya karance dukkanin Alkur’anin gaba daya. Haka kuma rayuwarsa take, duk tsawon rayuwarsa.
To, haka kuma za ka ga, wani sun ce masa babban gwarzo ne. Amma kuma lallai an sani a tarihi, shi gwarzon dannawa a guje ne a fagen fama. Ya gudu ba daya ba, ba biyu ba. Amma a rubuce wai shi Gwarzo ne. To, ina ake gwarzantaka? A ce gwarzo a yaki, amma bai taba yaki ba ma sam-sam, tunda yake. To, haka nan, sai ya zama mutane irin wannan. Da yake ana ta kokari ne a rufe ‘fada’il’ din Ahlul baiti.
Wannan zaunannen abu ne a kan cewa; da farko da suka dinga kirkiro ‘fada’il’ na wasu mutane, sai suka ga falalolin Ahlul baiti ya ki ya rufu. Sai suka ce, yadda za a yi, duk abin da aka samu na ruwaya wadda ta nuna wata ‘fadila’ ta Ahlul baiti, to, a kirkiro irin sa a ba sauran mutane. Ko kuma a ce wannan (su Ahlul baiti) ba su kebanta da shi ba, na kowa da kowa ne (na dukkan muminai ko na duk sahabbai). To, a kan wannan ginin aka zauna.
Mu kuma muka yi rashin sa’a, mu nan irin abin da ya zo mana kenan. Saboda haka sai ya zama abin da mutane suka sani dangane da Sayyida Zahra, ko ya zama ma kadan, ko ma ya zama ma ainihin, muna iya ce masa ma gurgudadde. Ko ya zama an fadi wani gurgudadde, an birkita shi sama a kasa, ko kuma ma ba su sani ba gaba daya. To, sai ya zama galibin abin da suka sani kawai kalilan. Na karatu kalilan ne. Ka san mutane sukan yi ta abubuwan su da baka, su yi ta fadi, wanda yake ba shi a littafi. Kamar nan kasar, akwai daukan garan Nana Fatima. Za ka ji suna ta labarin daukan garan ta. Har ma mata burinsu shi ne ranar alkiyama su dauki gara. Ko wa ya ce musu ana daukan garan? Amma haka aka gaya musu. Ko mutane suka kirkiro cewa za a dauki garan? Da yake su nan suna yayin daukan gara din, su kama hanya su je gidan Amarya. Ban san ko har yanzu ana yi ba. A kama hanya a tafi kai Amarya da kaya. Sai suka ce za su kai na Nana Fatima. Su suna fatan su yi haka nan ranar Alkiyama. Wato, ka ga Aljanna tsaf kenan! To, amma su san wani abu dangane da Sayyida Fatimatuz Zahra ba su sani ba.
To, saboda haka ya nuna a wannan muhalli, lokacin da mutane suka ga ana fitowa, suka ga tarin jama’a, za su ce; wai mene ne? Sai aka ce; ai ana murnar haihuwar Fatima ’Yar Manzon Allah ne. Sai su yi shiru, sai ya zaman musu bakon abu, ai ba su saba ana yi ba. Alhali in ana batun darajojin Sayyida Fatimatuz Zahra ne, ko da daraja guda daya rak. A ce ita ce; Uwar A’imma, ya wadace ta. Ballatana kuma a ce kuma, ah, ai kuma ita ’Yar Manzon Allah ce. Wanda Manzon Allah (S.A.W.W.) yake ce mata “Fatimatu bid’atun minni”, wato “bangarena ne.” Ta yiwu ka ce; bangare, ai haka ne, tunda ’Yarsa ce, jininsa ce. To, amma yadda ya fadi ‘bid’a’ din ya nuna cewa ba ‘bid’a’ na mujarradin jini ba ne. Inda ya ce “wanda ya fusata ta, ni ya fusata, wanda ya yarje mata, ni ya yarje ma.” Wannan ya koma a wani babi na daban. Domin wannan yana nufin kenan ko da bayan ba Manzon Allah, duk wanda ya fusata Fatima, ya fusata Babanta. Wanda ya fusata Babanta kuma ya fusata Allah. Sai kuma a wani ruwaya wanda duk suna da shi, wanda ya ce “yardar Allah yana tare da yardar Manzonsa, yardar Manzonsa yana tare da yardar Fatima. Fushin Allah yana tare da fushin Manzonsa, fushin Manzon kuma yana tare da fushin Fatima.” Wannan ya daran ma (sauran). Kuma za ka ce; to, wancan ‘bid’a’ kuma ne? Wannan kuma har akwai Allah a ciki.
Sai kuma wani ci gaba kuma, wanda ya zamo kai tsaye, ya ce ainihin “yardar Allah na tare da yardar Fatima.” Ba tare da ‘wasidan’ Annabi ba. “Fushin Allah na tare da fushin Fatima.” Wannan duk mai imani zai fahimci cewa; ashe Fatima din nan tana da wani matsayi ne na daban, ba mujarradin diya ta jini ga Manzon Rahma ba. Ko da diya ce ta jini, daraja ce. To, amma kuma sai aka nuna ita tana da wani matsayi ne.
Hatta in ya inganta, Manzon Allah yana da wasu ’ya’ya mata banda ita, yana da Zainab da Rukayya da Ummu Khulthum. Hatta in ya inganta yana da wadannan ’ya’ya. To, amma ba a ruwaito, an ce ita dayansu ita ma ‘bid’atul Mustafa’ din ba ce. Duk da yake ‘bid’a’ ce, in ya inganta ’yarsa ce a jini, amma ba a ruwaito shigen irin wannan ruwayar ba. Wanda zai nuna maka ashe ita wannan tana da wani matsayi ne na daban.
To, sai mutum ya yi tambaya, wannan matsayi, ya aka yi ta samu wannan matsayi ‘masalan’? Kamar yadda nake cewa; duk lokacin da aka yaba ma mutum, za ka ga ya yi wani abu ne wanda ya cancanci wannan yabon. Wato in Allah (T) ya ba mutum matsayi, sai ya ‘ahhala’ shi ga wannan matsayin. Kamar shi wannan Manzon shi ne, Fiyayyen halitta. Shi ne kuma Shugaban Manzanni. Don haka ne ma irin yadda aka aiko shi da wahalhalolin da ya sha da yadda al’amarin ya (tabbata), sai ya zama yafi na sauran.
Wahalarsa ta fi ta saura. Sannan sakonsa ya fi na saura. Sannan inda aka aike shi da kuma inda (ya rayu), sakonsa sai ya fi na saura. Wanda yake, ko da ko yanzu alal misali, za a ce ai akwai masu rayawar suna bin Isah rututu a doron kasa. Amma in mutum ya yi nazari da dikka, zai ga cewa; shi addinin da Isah din ya zo da shi, wanda yake albishir ne ga zuwan wannan Manzo, za ka ga ba shi suke bi ba, wani abin ne daban.
Amma ainihin inda za ka ce musu takamaime ina koyarwar shi Isah din? Ka kwatanta za ka nema ka rasa. Ko kuma za ka ga akwai karo, karo nan, karo nan, karo nan, in ma ainihin ka sa hankali, sai dai ya ruda ka kawai. Shi ya sa ma wasu idan suka sa hankali da zurfi, sukan zama kawai su dawo su ce; sam ma ba su yarda da addinin ba. Saboda irin ‘tanakulin’ da suka dinga gani a cikin koyarwar. Wanda yake ko, inda za su zo su ga koyarwar da wannan Manzon da ya zo da shi, su duba koyarwar Alkur’ani, sai su ga cewa, sun ga abu ya fita fes. Sun samu waraka. To, menene dangane da ita Sayyida Fatimatuz Zahra, wanda ainihin ya ‘ahhala’ ta ga wannan babban matsayi, baya ga ruwayoyi kawai? Domin in ruwayoyi ne, sai mu ce; gonar ruwayoyi, wadansu mutane ma an musu ruwayoyi, an ce su ma suna da darajoji ko? Kuma a hisabin wasu ma yana iya zama ya inganta. Duk da yake da yawansu ba su inganta ba, da dama daga ciki. Kusan ma muna iya cewa; galiban wadanda aka ruwaito din, yakan zama a wadansu littafan da suka dauki hululu din ne. Wadanda suke da shi ingantacce (wanda suka inganta din), to, sai kuma sun inganta wani wanda ya zo ya yi karo da shi. Sai su saraya gaba daya. Hankali ba zai karbe su ba. Amma wannan ko, za ka ga magana ta fita, ya inganta. To, mene ne ya ‘ahhala’ ta? Shi ne abin da muke kokarin mu ce.
To, da ta samu wannan babban daraja, ta samu ne saboda kawai mujarradin an fada? Ko kuwa yaya? To, ta nan ne ba su san Sayyida Fatimatuz Zahra ba. Tun daga haihuwarta da rayuwarta har ya zuwa wafatinta. Ta nan ne ba su san ta ba. Inda za ka ce, yi mana tarihin Sayyida Zahra. Na taba sauraro a wani tasha na talabijin, yana ba da tarihin mata a Musulunci. Suna yi, nan da nan su yi wannan su gama, su yi wannan su gama, su yi wannan su gama. To, sai na ga abubuwan da suka fadi dangane da wasu matan ma, sun dan dade suna fadan abubuwa wanda yake har ya fi ma na Sayyida Zahra yawa. Duk da sun fadi abubuwa da dama dangane da Sayyida Zahra din.
To, makasudin wannan buki namu, kun ga baya ga nuna murnar mu, ‘fi’ilan’ muna nuna murnarmu, ya kamata har wala yau kuma mu zakulo tarihi daidai gwargwado don mu tunatar da juna dangane da ita wannan Sayyida mai dimbin daraja, wanda zai sa mutane su fahimce ta, su san ita wace ce, su san kuma lallai ashe sun jahilce ta saboda ba su san abin da ya gudana da ita ba a rayuwarta.
To, ban san wannan lokaci ko zai ishe mu ba. Tunda yake mun dauki kwana uku ne kawai. Domin lokacin wafati an yi janibin wafati. Wannan karon mun sami kamar kwana hudu ma. Mun yi kwana uku a jere, mun zo kuma mun yi na ranar uku ga wata, kun ga mun samu kamar kwana hudu. Saboda haka wannan ya ba mu dama mun dan yi magana (kodayake) ba mu faifaye da shi ba. Amma mun dan yi da dan dama fiye da wanda muka saba yi da, wanda muke yi rana daya, ya zama mun takura sosai. To, wannan insha Allah da yake bukukuwa ne daban-daban, da abubuwa daban-daban, insha Allah daidai gwargwado za mu yi magana dangane da haihuwa din, haihuwarta ‘awwalan’. Sannan kuma rayuwarta tsakanin gobe ke nan zan ce, da jibi insha Allahul azim, da yake yanzu lokaci ya kure.
Da yake har wala yau wannan lokaci ne kuma da muka dauka ya zama na ’yan uwa mata ‘khasatan’, don haka ne ma su ne aka ba su alhakin tsara shi maulidin Sayyada Zahra din. Kuma akwai wani abu da Majalisar Dinkin Duniya sukan kirkira su ce Ranar Mata ta duniya. To, shi kenan, ‘falyakun’, a yadda suka sa irin nasu. Amma mu ba ranar da ta fi dacewa ta zama Ranar Mata ta duniya irin ranar haihuwar ‘Sayyadatu Nisa’il alamin’. Saboda haka mu a wurinmu ranar haihuwarta, ran nan ne Ranar Mata ta duniya.
Kuma in ana fadin wadansu abubuwa dangane da Sayyida Zahra, hatta wadanda suke ba musulmi ne ba su, za su sha mamakin a ce akwai irin Gwarzuwa irin wannan, shi ne su ba su taba sani ba? Ai ya kamata, da a ce an yi koyi da al’amarinta, ai ka ga da lafiya lau. To, insha Allah, da yake muna dan ‘mukaddima’ ne, don lokaci ya dan kure, za mu yi sallah, ‘awwalan’ yanzu. Bayan sallah, insha Allahu kuma, matayassara za a yi shi ma bayan sallah din. To, yanzu insha Allah, zan iya cewa na zama kamar mai dan gabatarwa maimakon mai jawabi. Don yanzu ba lacca din na yi ba tukunna. Na dan yi ‘mukaddima’ ne. Insha Allah bayan sallah wani abu zai biyo baya, sannan kuma tsakanin gobe da jibi, insha Allah, za mu dan tsattsakuro matayassara, insha Allah. Wasallallahu ala Muhammadin wa alihid dahirin.

wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua

comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.