Mahdiyanci da Mahadi

Mahdiyanci da Mahadi

Mahdiyanci da Mahadi

SHEIKH WA'ILI
Fasali Na Biyar

Daga Cikin Akidunmu Akwai Zuwan Imam Mahadi
Ban taba ganin wani littafi da aka rubuta a kan Shi'a ba face sai an rike Akidar su a kan Mahadi hanyar yi musu izgili, da kuntatawa kuma sannan a kirkirowa wannan akidar wasu tunanunnuka na gefe, kuma an sanya mata wasu munanan abubuwa wadanda suke tattare da ita, kuma sai ka ga marubucin ya zare makamin sa yana nuna cewa zancen sa na ilimi ne sannan ka ga yana kaiwa da komowa, kai ka ce ya fitar wani babban lamari, kama shi kadai ne wanda gagara badau, kuma sauran mutane wawaye ne, bari mu gani daga ina wannan tunanain ya zo kuma shin Shi'a sun rike shi ne daga ingantacce masadari na addini ko kuwa? Kuma a haka zamu tafi tare da akidar, wadanda su ka yi rubutu a kan Mahadi suna jingina ko danfara tushen wannan tunanun ko akidar da lamurori guda biyu, na daya shi ne kagaggen tunani, na biyu kuma akida ta addini, wadanda kuma su ka alakanta akida da kagaggen tunani su kuma sun kasu kaso biyu, kuma da sannu zamu ambaci maganganun su bisa bangaren da suka karkata zuwa gares shi, kuma suka rinjaya a kan cewa shi ne tushen wannan fikarar ko akidar.
1- Bangare na daya: Su ne wadanda suka jingina wannan tunanin zuwan Imam Mahadi da cewa tunanin kagagge a kan kansa, su na ganin cewa lalle bai kebanta da tunani shi'anci ko na musulmi ba kawai, kai ba ma kawai a kan addinan sama gaba daya ba kawai, abin har ma ya kai ga matakin al'umma, wannan kuma saboda abubuwan da ke cikin kuma su ke gudana a cikin dukkanin al'ummu, domin lamarin zuciya iri daya ne. Kuma shi ne jin cewa a cikin wani lamari wanda ba na daidai ba na daga hukuncin da yake ci a yanzu da kuma bakin ciki mai bibiyar juna daga mahukuntan da suka gabata zuwa wadanda suka shude, sun rayu tare da al'ummar su bisa yanayin wanda ya ke tilastawa da wanda ake tilastawa, da wanda ya ke salladuwa akan mutane da kuma wanda ake salladuwa akan su, kuma suka sanya su a karkashin wutar zalunci da girman kai, saboda haka ne wannan akidar ta zama a cikin kowace al'umma ta gabascin duniya dama makamantan ta, na daga wadanda suka cudanya tare da mutanen gabascin bisa cewa wannan abu ne mara tushe, abin watsarwa. Gama cewa sashin ma'abota wannan akidar suna yin riko da akida ta addini wacce ita ma tana yin bishara da Mahadi: To lalle ka ga wannan akidar mihimmancin ta ya bayyana ta bangaren cewa tana karfafar wannan kafaffiyar dabiar ta cikin zuciya, kuma ta haifar da wani yanayi da nau'i na shar'ancin wannan tunanin a cikin zukatan mutane, wannan ita ce Fassarar da Bartarand Sal ya fadi a nasa batun.
Dangane da al'amarin gasgata mafi yawa daga cikin akidodjin addini sababin sa ba ya komawa zuwa wani tsayayyen dalili wanda yake ingantacce, kamar yadda abin yake a cikin lamarin ilim ba, sai dai abin da yake jawo wannan shi ne tsammanin samun hutu na nan gaba wanda yake danfare da yakini, idan ko har yin imani da wani lamari ayyananne yana sa mu cimma abin da muke kwadayi ko mu ke so to ina fatan wannan lamarin ya zama ingantacce kuma daga baya ni ma sai na yarda da ingancin ta.
Ke nan gwargwadon da ya hada mutane a kan wannan shi ne yin gini a kan wannan burin na bayyanar mai kubutarwa daga mummunan yanayin da al'ummu suke rayuwa a cikin sa. A kan wannan Dakta Ahmad Ahmad Mahmud yake cewa:
Lalle akidantuwa da bayyanar Isa ko sauraron dawowar mai kubutar wa wannan abu ne da hankalin gungun mutane ya haifar da shi, a cikin jama'u ko al'ummu da suke yin tunani irin na su kiradiyya a cikin lamuran su na siyasa, haka ma al'ummar da ta sha kaifin zalunci, ta kuma kasance akarkashin wutar dagawa, daidai ne daga sarakunan su ne ko kuma daga masu kawo musu hari daga cikin wadanda ba yan'uwan su ba, lalle a daura da zaluncin sarki a cikin tunanin addini burace-burace da suke ratayuwa da zukata na mai kubutarwa, ko mai yan'tarwa wanda zai cika duniya da adalci da daidaito kamar yadda ta cika da zalunci da rashin daidaito.
Ke nan duk da cewa akwai masdarori na addini a cikin litattafan Yahudawa da nasarawa a kan wannan akaidar sai dai cewa wadannan masdarorin ba sune tushe na asali a gare su a mahangar wadannan mutanen ba, kadai dai kawai tana taka rawa ne a karo na biyu a wajen bada mafita, kuma Dakta Ahmad Mahmud ya na ganin cewa lalle akidar Sunna ta yin hakuri da kuma rashin yi wa sarki tawaye ta tauye lamarin ruruta lamarin Mahadi da kuma tabbatar akidar addini ta Sunna a kan matsakaicin lamari, ta yadda suka yarda su rayu a tsakanin abin da ke tayar musu da buri, na daga barna da lalacewa ta sarari da su kai ta sha a kwanakin umayyawa da abin da ya biyo bayansu, da kuma tsakanin burin kubuta daga wannan yanayin, sai ya karkata zuwa jiran lokacin kubuta mafi nisa, kamar yadda ya samu a cikin akidar Mahadi, kuma lalle ya yi kokarin ya sa Shi'a a cikin wannan la'akari da cewa suna da hakuri a kan zalunci.
Lalle wannan akidar ba wanda zai yi imani da ita sai wadannan da suka fama da tashi in fadin tunani da zuci sakamakon yadda suke kin ayyukan da mahukunta suke yi da kuma yadda suke ganin cewa ba su cancanci su zama mahukuntan ba, saboda fasikancin su, da kuma sakamakon rusunawarsu ta wani bangaren a gaban gaskiya, saboda tsoron fatina kamar yadda a bin yake a wajen Sunna wadanda ba su da ra'ayin yin fito na fito da azzaluman shuwagabanni bisa dogaro da wasu hadisai da suke a wajen su, ko kuma sakamakon jin rashin iya yin motsin kamar yadda motsin da yawa daga cikin masu neman yanci ya sami tasgaro, kamar yaddda lamarin yake a wajen Shi'a wadanda suka tafi a kan yin hakuri da halifofi bisa takiyya, don haka akidar Mahadi ta samo asalin ta ne daga wannan tashi in fadin, amma mazhaboin da suke ganin cewa yin umarni dakyakykyawa da hani daga mummuna daya ne daga cikin tushen addinin su kamar hawarijawa da zaidiyyawa: Lalle wannan akidar ba tada wajen zama, har dai zuwa inda yake cewa: Sadoda mahimmancin Mahadi a wajen Shi'a masu Imamai sha biyu ba zai taba zama daidai da wanin su ba daga cikin mazhabobi, wadanda matakin da suka dauka a kan halifofi ya zama na daban kamar dai yadda suke ganin haramcin yin fito na fito da sarakuna ta daya bangaren. Wannan shi ne takaitaccen bayanin da duktar Ahamd Mahmud ya fadi, kuma muna da wasu `yan mahangogi da tsokaci masu zuwa a kan wannan fasalin.

1- Tsokaci na farko:
Lalle wannan cakudedeniya ce tsakanin sababi da sakamakon sa, wannan kuwa saboda al'ummun da suke cakude da addinai a jumillance zaka ga a bayyane sun hadu a akidojin su na addini, idan har ba a samu masdari na addini daga wannan yanayin ba, to a wannan lokacin wani dalili ne na daban ke nan, babu makawa wadannan addinann guda uku sun yi bushara da al'amarin mai kubutarwa ko mai tsamarwa kuma shi shugaba ne guda daya ga kowa da kowa wanda Allah zai hada kan addinai da shi domin ya kubutar da su daga zalunci, ko kuma ya zama daban daban, kowace al'umma da ga cikin al'ummu tana da nata mai kubutarwar (Mahdin) ta, kuma hadafin zawan sa da kuma yin bushara da shi, shi ne a fitarwa kowace al'umma misali babba da zai zo ya kamanta kalmar nan ta adalci kuma dan al'ummu su zama da alaka ta kai tsaye tare da kyakkyawar fikirar nan zababbiya ta wannan mafi kyan misalin kamar yadda ake surantawa, lalle asalin fikirar Imam Mahadi nassosi ne na addini, kuma bikatuwar ruhi zuwa gare ta ya taimaka a wajen kafuwar ta a cikin zuciya, musamman idan baza ka iya kamanta adalci ba saboda wani dalili. Sai dai cewa, a kan yi amfani da wannan lamarin na Mahadi domin cimma wani hadafi na daban, shi ne ya zama wata Katanga da a ke amfani da ita wajen hana yin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna musamman idan nassosin addini saka tsaya a kan darowa dan Adam nauyin kare kansa da kuma tsarkakan abubuwan sa na addini ba tare da ganin tsayawar Imam Mahadi da kuma rashin tsayawr sa ba kamar yadda yake tabba sa ckin koyarwar addini, don haka bai kamata ba fikairar Imam Mandi ta tashi daga matsayin tan a sanya misali madaukaki, da kuma bayyana hanyoyin daukaka, zuwa wani abin ban tsoro da yake kashe hankoron zuciya da mazantaka ba, ko kuma ya zama dalilin da zai sa mutane barci ba.

2- Tsokaci na biyu:
Lalle hada Shi'a da Sunna waje guda da cewa ba sa tsayawa a gaban azzalumi saboda takiyya rodani ne a sarari, wannan kuwa saboda dalilin da ya sa Sunna sake yin hakuri a kan zalunci dalili ne na bisa zabi, sakamakon rukon su da hadisan da suke ganin ciwa ingantattu ne, yayin da hakurin Shi'a a kan zalunci sakamako ne na yanayi da ya tilasta su saboda rashin samun damar mutsawa, kuma wannan yanayi ne gamamme a wajen dukkanin mutane, amma da an samu sababan motsawa Shi'a ba za su jira bayyanar Imam Mahadi ba domin ya zo ya kawo musu gyara ba, bisa sharadin cewa lalle hukuncin umarni da kyakkywa da hani da mummuna sharadi ne tsayayye akowane lokaci, haka ma jihadi da dukkanin kashe- kashen sa, ta hanyar samuwar mataimakin Imami na musamman ko na baki daya, a ra'ayin wasu malamai wannan izinin har yanzu yana nan amma kare kai daga azzalumi da tsarkakan abubuwa ba a shardanta musu samuwar Imami ko mataimakin sa ba, bisa ra'ayin jamhuru fakihan Shi'a, domin kare kai ne kuma wajibi ne mutum ya tsaya da wannan a kowane lokaci daga cikin lokuta.
Lalle kumawa zuwa tarihi Shi'a zai bayyanar da tsayayyun dalilai a kan abin da muka ambata saboda yawaitar yin tawayen su a kan barna a cikin zamanoni mabambanta da kuma yin jihadi tare da sauran Musulmai a cikin fagen jihadi tare kafirai da zalunci kuma bani da bukatuwa zuwa in tsawaita saboda kasantuwar abin a fili.
3- Tsokaci na uku:
Dalilin kadaitakar sababi ba zai sa al'ummu su hadu a kan akidar Mahadi ba saboda muna ganin da yawa daga cikin mabayyana halayya daidai ne ta kasance halayya ce ta addini ko kuma al'umma ba su yi tarayya a kan ta ba kuma ba tare da kasantuwar zuwan ta daga illa guda daya ba, daukin misalin lamarin gabatar da kurbani lalle a wajen ma'abota addinan sama wata alamace wadda ake neman kaucewa fushin ubangijoji da ita, a wajen wasu kuma domin kore ruhi masharranci, a wajen wasu kuma ana gabatar da layyar dan Adam ne domin riskar alheri kamar yadda yake a waje mutanen kasar Masar na da, dalilin bai zama kala daya ba kamar yadda kake gani, ke nan zai yi yu mahangar lamarin Imam Mahadi ta zama ba abu ne na neman sauyi ko samun hutu ba, kadai wannan fikra ce da ta kafa wata alama ko Katanga da zata dawwama a matsayin yar manuniya a ko da yaushe da zata rika tunawa mutane da cewa lalle azzalumi ana jinkirta masa ne amma fa ba za 'a ce jinkirta masa aka yi ba idan mutane suka yi sakaci wajen neman hakkin su ba, kuma sama ba za ta saurara ba a wannan lokacin don haka babu makawa da a dauki fansa a hannunta, hannun mai kubutarwar tare da la'kari da cewa lalle asali a cikin misalin irin wadannan yanayoyin mutane su yi tsayin daka domin magance karkacewa daga tafarki don haka ne ma Allah yake cewa "Lalle Allah bay a canja abind ke ga mutane har sai sun cenja abin da ke yanayin su" Ra'adi / 12. idan sakaci ya yi rinjaye a kan su lalle Allah Madaukaki ba zai jinkirta lamarin bayin sa ba don haka ne ma wannan a yar mai girma ta ke yin nuni a cikin fadinsa madaukaki: "Har sai lokacin da manzanni suka yenke kauna kuma suka yi tsammanin an karyata su sai taimakon mu ya zo musu sai mu kubutar da wanda muka ga dama kuma ba mai iya kawar da azabar mu daga mutane masu laifi" Yusif/ 110. kuma masu fassara sun yi kai kawo a kan fassarar wannan ayar a kan ma'anar da muka ambata, kuma suka fadi cewa lalle sama tana sa hannu yayin da bala'i ya tsawaita kuma yanayin ya tsananta sannan mutane suka kusa kaiwa zuwa haddin yanke kauna.

2 - Bangare na biyu:
Wadanda suka alakanta fikirar Imam Mahadi da cewa an riko da al'ada ne, suke ce lalle wani iktibasi ne da musulmi suka rika daga sashin al'ummu ba tare da cewa akwai wani tasiri na shu'uri wanda ya hada tsakani ba, kuma daidai ne an riki wannan akidar daga wannan al'ummar ce ko waccen jaular Tusaihar da kuma dokar Falaton `yan yammacin duniya sun ce: An ciro ta ne daga Yahudawa da wannan shakali ko kuma wani shakalin na daban, kuma Falaton yana karfafa cewa wannan ruwayar ta zo ne daga cikin abin da Ka'abul akhbar yake ba da labari, shi da Wahab dan Munabbah, kuma lalle tana daga cikin irin tunanin na isra'iliyyancin da suka yadu tsakanin Musulmai, a yayin Ahmad alkasrawi ya tafi a kan cewa an cirato tan e daga farisawa, a inda yake cewa:
Ba boyayye ba ne cewa mutanen farisa na da sun tafi a kan Allahn alheri wanda ake kiran sa Ahrumain, kuma suna raya cewa lalle ba su gusheba suna hukunta kasa, har sai Sawashiyanat dan Annabi Zaradahsat ya tashi ko ya bayyana sai ya ci nasara a kan ahramain sannan duniya ta ciki da alheri, wannan akidar ta yi tasiri a cikinsu, yayin da Musulumci ya bayyana kuma Musulmai suka bude Irak da Iran suka cakuda da Iraniyawa sai wannan akidar ta yi naso daga cikinsu zuwa Musulmai, kuma yaduwar ta zamo cikin gaggawa mai ban mamaki. Kuma ba mu da masaniya ku sheda a kan kalmar Mahadi kuma ba mu san waye ya kire ta ba, kuma yaushe aka kire ta? wannan ne karshen maganar a takaice .
Lalle wannan ra'ayin a gaskiya bai bukatar wata tattaunawa, saboda dalilai masu zuwa, daga ciki akwai cewa rayawarsa cewa Musulmai sun yi sakaci wajen ta yadda suka zamo suna akidantuwa da lamuran da ba su san masdarinsu ba, daga cikin akwai rashin samun wata alaka tsakanin fikirar alheri da na sharri da kuma lamarin mai tsamarwa mai ceto daga ciki akwai cewa lalle girman mas'alar Mahadi ba haka take ba.
3- Bangare Na Uku:
Alakanta fikirar Mahadi da kirkirarren tunani, da munafa ta siyasa, ma'abota wannan fikirar suna ganin cewa lalle tunanin zuwan Mahadi sashin yan siyasan da suka yi mulki wadanda ba su da cancanta ne suka kirkire ta wadanda Musulmai su ke ganin ba su cancanci shugabanci ba, sai suka kirkiri cewa akwai wani shugaba da boyyayye mai yantarwa kuma da sannu zai bayyana wani lokaci, kuma lalle ya yi musu alkawari tsayawa da hukunci har zuwa lokacin da zai bayyana. Kuma su ka ce lalle Mukhtarus Sakafi yana daga cikin wadanda suka bi wannan tafarkin kuma ya yi da'awar cewa Mahadi daga cikin alayen Muhammad ne ya wakilta shi. Daga cikin wadanda suka tafi a kan wannan ra'ayin akwai malamin nan na yammacin duniya wat , kuma wannan ra'ayin yana wanzar da tasirinsa a wajen da yake yin tasiri, wadanda suka riki fikirar Mahadi majingina a gare su bisa tabbacin cewa suna da yawa, babu makawa tunanni a kan Imam Mahadi ya zam ya yadu a tsakanin mutane tun kafin zamanin su, sai suka amfana da wannan damar su ka hau doron bayan akidar bisa cewa jingina wannan ra'ayin ga mukhtar la'akari da cewa shi wane jego ne na akidar kaisiyaniyya wanda da yawa daga cikin muhakkikai sun karyata shi, kuma tare da tabbacin cewa lalle wannan akaidarsamammiya ce kafin zuwan sa kamar yadda muka ambata a baya, kuma mukhtar ba shi da wannan matsayin mai girma a wajen Musulmai da zasu riki ra'ayin sa kuma su tasirantu da shi, tare da waiwayawar Musulmai bisa hadafin sa.
?
Akidar Musulmai a Bisa Lamarin Mahadi
Lalle fikirar Mahadi a cikin lamarin akidar addidni tare da rashin waiwayawa zuwa bayanin ta dalla-dalla, mahalli ne na ittifakin jamhurun Musulmai, ruwayoyin da suka zo a kan Mahadi da kuma sauraron yayewa a hannun sa da kuma bayyanar sa domin ya cika duniya da adalci kamar yadda ta cika da zalunci, sun zo a cikin litattafan kowanne daga cikin Shi'a da Sunna, daga cikin abin da Imaman Ahlus-sunna suka ruwaito akwai:
Imam Ahmad a cikin masnadinsa, da kuma Turmuzi a cikin sunan din sa da kuma abu Dauda a cikin sunan din sa da kuma Ibn Majah a cikin sunan dinsa da kuma Hakim a cikin mustadrak dinsa da kuma kunji bashafi'e a cikin littafinsa Albayan fi akhbari sahibul zaman da kuma Ibn Hajarul Askalni a cikin Al'kaulul mukhtasar fi alamatul Mahadi Almuntazar da da kuma Yusif dan yahya da kuma Badamashke a cikin Akadur durar fi akhbari Imam almuntazar, Haka ma Ahmad dan Abdullah Abu Na'im ma'abocin littafin Hilyatun fi na'atil Mahadi da kuma Muhammad dan Ibrahim al'hamawi a cikin mishkatul masabih da kuma Samhudi a cikin Jawahirul akida da ma gomomi daga cikin gagga- gaggan malaman Sunna da makamancin su. Kuma ba na so in tsawaita a wajen ambaton su.
Masana ilimin hadisi sun fitar da hadisan Mahadi daga Imam Ali (a.s) da dan Abbas da Abdullahi dan Umar da Dalhat da dan Mas'ud da Abi Hurairah da Abu Saidul Khudri da kuma Ummu salma da makamantan su,
Daga cikin wadannan hadisan akwai abin da Ibn Umar ya rawairto da sunan dinsa daga Annabi (s.a.w) "A karshe zamani wani mutum daga ahli na zai fito sanan sa irin sunana kuma alkunyar sa irin alkunya ta, zai cika duniya da adalci kamar yadda ta cika da zalunci, wannan shi ne Mahadi" haka ma kamar fadin Manzo (s.a.w): " Mahadi daga cikin `ya`yan Fatima yake". Kuma Ibn Taimiyya ya inganta wadannan hadisan da makamancin su, wadanda suka zo a kan Imam Mahadi, yana mai jingina zuwa Musnadin Ahmad dan Hambali da Sahihi Turmuzi da kuma sunanu Abu Dauda.
Ibn Hajar ya tafi a kan kafirtar wanda ya musanta samuwar Mahadi bisa dagaro da nassosin da suka tabbatar da samuwar sa, ya bada amsa a cikin Fatawal Hadis yayin da a kan tambaye shi a kan wadanda suke musanta zuwan Imam Mahadi, sai ya ce"Wadanda suke musanta zuwan mahdin da aka yi alkawarin bayyanar sa a karshen zamani bayan ya riga ya gabata a cikin hadisin da yazo daga Abubakarul Iskafi daga Manzo cewa wanda ya karyata zuwa dujjal ya kafirta kuma wanda ya kayata Mahadi ya kafirta har inda yake cewa kuma da sannu za mu jero masa hadisan da suke karyata wadannan kuma suke tabbatar da kaucewar su daga tafarki da kuma fasikantar da su, abin da yake a cikin sa akwai isarwa da kuma gamsarwa ga wanda ya yi tunani". Abu na'im ya fitar daga Manzo cewa: Mahadi zai bayyana alhali a kan sa akwi rawani tare da shi akwai mai shela yana yin shela cewa wannan ne halifan Allah ku yi masa biyayya". Sannan ya rika ruwaito hadisan da suka zo a kan Imam Mahadi (a.s), wannan sashin ruwayoyin da suka zo daga bangaren Sunna ke nan, amma ta bangaren Shi'a, ruwayoyin su a kan Imam Mahadi ta kowane bangare suna da yawa kuma sun zo ne daga Annabi (s.a.w) da kuma Ahlul-baiti (a.s) kuma sun wallafa litattafai masu yawa a kan wannan lamarin wadanda suka gamsar kuma suka amsa dukkanin tambayoyin a kan Imam Mahadi: Irin su littafin Gaiba na Muhammad dan Ibrahim Annu'umani da kuma littafin Kamalud din nan, Wa tamamul ni'imat na Muhammad dan Ali bin Babawaihil Kummi, da kuma littafin Gaiba na Muhammad dan Hasan Addusi, da ma makamantan su daga cikin wadanda suka yi rubutu a kan wannan maudhu'in kuma lalle kowanne daga Sudduk a cikin Ilalul shara'i'i da kuma Murtadha a cikin Tanzihil anbiya da kuma Majlisi a cikin Bihar da kuma da Mufid a cikin Fusulul muhimma, haka ma a cikin al'irshad, daga cikin mutanen baya-bayan ma akwai gamomin litattafan da aka wallafa a kan Mahadi kuma sun kosar da maudhu'in. kuma sun bijiro da dalilai a kan lamarin Mahadi kuma sun ambaci dalilai guda biyu kawai daga ciki:
1- Daga cikin dalilan da suka kawo na hankali shine dalilin ludufi, kuma abin da wannan dalilin yake nufi shi ne: Hakaki hankali yana yin hukunci da cewa wajibi ne Allah ya yi ludufi, shi ne ya yi abin da zai kusanta mutum da biyayya ya kuma nisanta shi daga sabo ya kuma tabbatar da koruwar dukkanin wani dalili ya kuma yanke uzuri ta yadda lamarin ba zai kai ga a jinginawa Allah takaitawa ba, don kada har ya zama mutune su na da hujja a kan Allah kamar yadda hankai ya yi hukunci da wajabcin aiko manzanni, da kuma tayar da Annabawa domin su bayyanawa mutanre abin da Allah ya saukar musu kuma domin su yi hukunci da adalci a tsakanin mutane, haka ma ya wajaba a sanya Imami domin ya tsaya a matsayar su, domin ya tabbatar da ainihin dallilin da ya sa aka aiko manzanni, domin lalle Allah ba zai bar doron kasa ba tare dah ujja ba, kuma babau wani zamani da yafi wani zamani cancantar wannan har dai zuwa karshen abin da su ka ambata.
2- Amma dalilai na nakali, daga ciki sun ambaci cewa abububwa masu zuwa: Allah Madaukaki ya ce: "Allah ya yi wa wadanda suka imani kuma suka yi aiki ha gari cewa lalle zai sanya su halifofi a doron kasa kamar yadda ya halifantar da wadanda su ka gabace su kuma lalle zai tabbatar musu addinin na su da ya yardar musu da shi" Imam Assadik ya fassara wannan ayar da fitowar ko bayyanar Mahadi kuma wannan ayar zata bayyana a hannunsa, wasu sun ce harshen wannan ayar gamamme ne kuma yana yin nuni zuwa tabbatar wannan lamarin a hannun Musulmai. Sai a kan amsa musu da cewa lalle dukkani alamu suna nuna cewa wadannan lamuran ba su tabbata ba, bisa yanayin da wannan ayar ta ambace su ba, tun daga zuwan Musulumci har zuwa ranar mu wannan, kuma alkawarin Allah babu makawa da ya cika kuma wannan hujja ce a kan cewa nan gaba zai tabbata karin a kan cewa lalle yana daga cikin salon da Kur'ani, yin magana a kan wani abu na musamman amma yana nufin gammemmen abu, ku kuma a kan mufradi (guda daya) a mahallin jam'i, a wurare da daman gaske, saboda haka ne ma Fakhrur Razi yake fada a yayin da ya ke fassara fadin madaukaki, " Ya ku wadanda ku ka yi imani duk wanda ya yi ridda daga addinin sa daga cikin ku to da sannu Allah zai zo da wasu mutane da ya ke son su kuma suke son sa masu kaskan da kai ga muminai masu izza ga kafirai wadanda suke yin jihadi a tafrkin Allah ba sa jin tsaro zargin mai zaigi" har dai karshen ayar.
Sai ya ce ayar ta sauka a kan Abi baker bisa dalilin cewa shi ne wanda ya yaki wadanda suka ridda tare da cewa hashen ayar gamamme ne, kuma daga ciki hadisan da Shi'a suka kafa hujja dasu a kan lamarin Mahadi akwai Hadisin da Dusi ya rawaiti shi a cikin littafinsa Algaiba, wannan fikira ce takaitacciya da na so in yi nuni zuwa haduwar Musulmai a lokacin Mahadi, a wannan lokacin, zancen wadannan mautane wadanda suke nisanta wannan tunanin da ga Musulumci tare da yin ko oho da abin da yazo na daga tushe mai karfi da nassosin wannnan addinin, zai zama ba shi da wata kima. Kuma idan ma har wasu sun ci gajiyar wannan tunanin a tsawon tarihi ai wannan ba zai zama dalilin musa fikira da kuma jifan wanda yake akidantuwa da ita da bin rudani ba. Ya tsananin saukin yin jifa da wani ra'ayi idan ya zama bai yi daidai da maslahar mutum ko in ya jahilci shi ba!. Duk da cewa ba na inganta dunkkanin abin da ke tattre da lamarin na daga abubuwa na gefe, balle ma dole ne mu takaita a kan abin da ya inganta ta ingantattun hanyoyi, kuma lalle ya kamata wasu mutane su nisanci wannan maganar mai ban dariya, lamarin da ya kai wasu ga fadin:
Lokaci bai yi ga gidan karkashin kasa da haifo wannan da*
* Ku ka maishe shi dan Adam bisa zaton ku ba.
Lalle daidaituwa/mutuwa ta tabbata ga hankulan ku*
* Kun halitto wa mikiya da gilana na ukun su.
Lalle wadannan sun yi gaggawa har ta kai su ga fadin abin da ba su sani ba, amma mu abin da zamu iya cewa da wadannan shi ne salam kamar yadda Kur'ani ya yi umarni da hakan.
?
Kyakkyawan Sakamakon da ke Cikin Akidar Mahadi
Abin da ya rage shi ne mu san mene ne amfani akidantuwar mu da samuwar Mahadi, domin lalle daidaita irin wadannan lamuran zasu gyara da yawa daga cikin tunanunnuka na kuskure daga misalsalin irin wadannan akidun musamman idan muka san cewa lalle akida ita ce ke sarrafa zukata.
1- Sakamako na farko:
Amfani na farko da wannan akidar take da shi kamanta umarnin Allah Madaukaki da wannan akidar kamar dai sauran akidu, domin abin da yake tabbatacce shi ne ya wajaba a yi imani da nassosi kamar yadda muka fadi ra'ayoyin malamai a kan wannan.
2- Sakamako na biyu:
Jin cewa lalle akwai hujjar Allah a tsaye a cikin mutane ta hanyar samuwar Imami, domin da a ce an wadatu da wanda ba shi ba da ba a sami sabani tsakanin Musulmai ba, idan aka ce ai sabanin akan kansa yake faruwa, sai mu ce; lalle sabanin ya faru ne saboda rashin yin riko da Imamancin sa, kari a kan cewa mutum zai rika fuskantar rashin samin mafita a cikin ra'ayoyin malamai saboda samuwar Imami a cikin su ko da kuwa ba su san shi ba.
3- Sakamako na uku:
Samuwar Mahadi akwai ludufi na Allah Madaukaki da bayin Allah suke kusantar sa da shi, saboda yadda suke jin cewa Allah na nan na yin shirye- shiryen tsayar da adalci da kuma kawar da zalunci, idan kuma aka ce kawar da zalunci da bukatar ya zama bisa sababai na dabi'a daga bangaren mutane, sai a ce lalle wannan ingantacce ne, amma idan suka yi sakaci a kan wannan babu makawa Allah madaukaki zai shigarwa wadanda suka yi imani, idan kuma aka ce ai wannan zai faru ne alahira, sai a ce; misali wannan misalin tsayar da hukunce- hukunce ne aduniya (hudud) ko (haddodi) tare da cewa mai laifi ba za a bar shi ba a lahira, wadannan su ne sashin amfanunnukan da ke kunshe a cikin lamarin Imam Mahadi, muka ba wadannan ne dalili n aasali ba balle ma hikimomin samuwar sa ne kuma akwai wasu fa'idoji na daban wadanda manya- manyan litattafai suka ambace su, kuma suke gamsar da bangarorin mas'alar, zai iya yiyuwa a koma zuwa gare su.
?
Mummunan Sakamako A Ciki Akidar Mahadi
1- Sakamako na farko:
Mummunan sakamako na farko da wannan akidar take da shi, shi ne tana hana mutum tsayawa da abin da ya wajaba a kan sa, kuma tana sawa mutun tsoro ta kuma bar shi a matsaraici kaskantacce yana sauraron bayyanar Imam Mahadi domin ya karbar masa hakkinsa, wasun su sun suranta yadda Shi'a suka tsananta wajen nuna damuwar su a kan sauraron bayyanar sa, bisa cewa wasu daga cikin `yan Shi'a ba sa yin salla saboda tsoron kada Imam ya bayyana alhali sun shagaltu da salla sai ya zama ba zasu iya riskar sa ba, lalle wannan tsammanin abin wurgarwa ne, a dunkule da kuma dalla-dalla.
Bana bukatar yawaita magana a kan lamarin ballantana ma zan jingina wannan lamarin zuwa litattafan fikihun imamiyya, domin lalle jihadi da umarni da kyakkyuawa da hani daga mummuna da wajabcin kare kai a tsaya suke a kowane lokaci kuma ba su damfara da Imam Mahadi ba, daga na nesa ko na kusa ba, kuma duk wanda ya yi da'awa sabanin haka to ya nuna mana matsamar wannan hukuncin, amma kiraye- kirayen nan da suke ababan wurgarwa da kuma maganganun marasa ma'ana ababan wurgawa ne zuwa mafadin su kuma shi ne wanda ya fi cancantar su, dun wanda ya jefi mumini da abin da baya cikin sa Allah ya isa masa mai kiyayewa daga wannan jifan, kamar yadda hadisin Annabi madaukaki yake fadi.
2- Sakamako Na Biyu:
Yin imani da lamarin Imam Mahadi yana buga kwakwalwa sadoda abin da ke cikin wannan na daga abubuwan da ke da wahalar faruwa na daga kamar su tsawon rayuwa wanda ba a saba da shi ba, da boyuwa daga idanu da rashin samun wata fa'ida daga imamin da yake a irin wannan yanayin. Amsar wannan atakaice shi ne; lalle Shi'a ba sa sa wannan tsawon lokacin a matsayin lamarin da yake na dabi'a, kadai suna ganin sa a matsayin mu'ujiza domin suna fadin abin da ya tabbata na daga dalilan samuwar sa da kuma buyuwar sa da kuma alkawarin bayyanar sa, a irin wannan halin babu makawa mutun ya yi imani da hakan kari a kan rashin yiwuwar wani zamani ya wofinta daga Imamin da ya wajaba a yi masa biyayya, gini a kan haka, lalle samuwar sa mu'ujiza ce wannan zai sa maganar ta koma kan lamarin mu'ujizozi, kamar wani gamamme lamari dake magana a kan mu`ujiza kawai, kodai a gasgata ko kuma akaryata, idan kuma har muka karyata ta to mun karyata abin da yake tabbatacce a cikin Musulumci, amma mutum ya ce baya ganin haka wannan kuma ba sananne ba ne, balle ma ya halatta mutum ya zama yana da wani ra'ayi amma baida masaniya, kuma a kan yi amfani da ra'ayoyin sa, domin yana yin tarayya da mutane a cikin ra'ayoyi, kuma ya kan iya cin karo da ra'ayoyi sahihai. Zancen ya yi saura a kan rahin bayyana sababin boyuwar sa, ya tsananin yawan akidoji da hukunce- hukuncen da bama samun wani dalili a kan yin su, kamar irin jifa a cikin aikin hajji da sassarfa da kuma daukewar mace ga namiji nauyin da yakai na rabin diyya da kuma kirga adadin raka'oin sallah da makamancin haka, haka ma da yawa daga cikin akidoji.
3- Sakamako na uku:
Cakudedeniyar da ke faruwa ta bangaren samuwar Imami da kuma da yi masa biyayya ya wajaba da kuma kasantuwar sa baya yin hukunci, da kuma samuwar wani wanda yake yin hukunci kuma bai wajaba a yi masa biyayya ba, amsa ana shi ne lalle fakihan imamayya a tattare a lokacin gaibar Imam sana tabbatarda hukumar mai hukunci mai adalci wanda ya ke kiyaye maslahohin Musulmai kuma suke kare iyakokin su kuma suke yawar, yakar makiyan su kuma ya ke kiyaye matakan shari'a a cikin ayyukan sa a tattare.
Amma bayan wannan yar takaitacciyar masaniyar akan lamarin Imam Mahadi, ina so in tunantar da wadanda suke yin rubutu a kan ta, ta yadda zaka ga suna suranta cewa Shi'a kamar wasu mutane ne da suka riki hukunce-hukuncen su daga Kisra da Kaisar, tare da yawaitar abin da muka gangaro da shi na daga Hadisai danagane da lamarin Imam Mahadi, shin zai yalwaci/isarwa wani Musulmin da ya yi imani da Allah su musanta wannan ko kuma ya wurgar da ita cen nesa daga Musulumci, sai dai kuma in a ce lalle hadisan Mahadi Shi'a ne suka dasa su a cikin Litattafai sannan kamar yadda aka fadin hakan a kan wasu abubuwan na daban, tabbas idan ka kafawa wani hujja da wani hadisi sai kaga ya fadi hakan, don haka ya zam wajibi mu yi jifa da dukkanin litattafan da maka gada a cikin kogi, idan har zasu yardar mana da wannan tasawwurin, kuma babu wani tasiri na yarda da sakaknkancewa da zai yi saura ba, saboda munin idnuwa da hangen mutanen da ba sa karnar su sallama a gaban gaskiya, kuma yake fama da razani da firgici a duk lokacin da yaga sabaninda ke tsakanin Musulmai zai dinke, lalle muna yin kira zuwa ga yin riko da abin da Kur'ani ya shelanta: "Lalle wannan ce al'ummarku al'umma guda daya kuma ni ne ubangijin ku lalle ku bauta mini" Al,anbiya'u /92. ya tsananin kyan wannan nuniya ta Kur'ani na yin umarni da bautar Allah bayan da ya fara yin umarni da hadin kai, a cikin wannan ayar akwai nuni a kan cewa lalle da yawa daga cikin mutane yana yi musu wuya su yarda da hadin kai, saboda maslahar su ta duniya da ke cikin rarraba, kuma saboda wasu butum butumaye da bangaranci da yake cikin kwakwalen su da suke bauta musu, alhali Allah ya umarce su da su wargar da ita kuma su bauta masa shi kadai domin ya dunkule al'umma waje daya kuma ya daure ta (ya hade ta) da kalmar tauhidi.
Haidar Center for Islamic Propagation
Face Book: Haidar Center
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Monday, December 10, 2012

comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.