Mazhaba da Larabawa

Mazhaba da LarabawaMazhaba da Larabawa

SHEIKH WA'ILI
Fasali Na Hudu

Tattannawa a kan Littafin Nash'atul Ara'ab Wal-mazahib
Marubucin littafin Dakta Yahaya Hashim Fargal yana mai nufatar lamarin ismar imamai: Lalle ismar imamanci ta bayyana ne a wajen gullat, an ce lalle Zaidu dan Ali ya kasance yana musanta ta, sannan sai ya kai ga fitar da sakamakon cewa Sunna sun yi bahasi a kan ismar Annanbawa ne saboda Shi'a sun yi bahasi a kan ismar imamai, sannan sai ya ambaci hujjojin ismar imamai daga ciki akwai hadisin sakalain:
Lalle na bar muku abin da mutukar kun yi riko da shi ba zaku taba bacewa a baya na ba. Littafin Allah igiya ce wacce take nade da sama zuwa kasa da kuma yayan gida na, kuma ba zasu taba rabuwa ba har sai sun same ni a tafki, ku yi duba zuwa yadda zaku wakilce ni a cikinsu, sannan sai suka ambaci wasu kalolin na wannan hadisin, sannan sai ya ce: Wannan hadisin ya sanya `ya`yan gidan Manzo a matsayin Kur'ani kuma kwatankwacinsa kamar yadda ya sanya musu dukkanin matsayin da Annabi yake da shi na daga matsayi da martaba, in banda Annabta, domin ya zama kamar yana nan ne shi da kansa domin ya tsaya da kiyaye shari'a, wannan hadisin ya ajiye `ya`yan gidan Manzo a matsayin Kur'ani ka ga ke nan babu makawa da ya zamo a tare da su a kan dukkanin abin da yake cikin sa na daga ilimi, daga nan Imami zai zama masani dukkanin Kur'ani da Sunna dalla-dalla domin a riki ilimin su daga gare shi a kammale sannan ya gabato da ruwayoyi na Shi'a dangane da ilimin Imami daga ciki akwai abin da ya zo daga Imam Ali (a.s) ba a saukar da wata aya daga Alkur'anin ga Manzo ba face sai ya karanta mini ita ya yi tilawar ta a gare ni kuma na rubuta ta da hannuna kuma ya sanar da ni fassararta da ta'awilinta da muhkamin ta da mutashabihin ta da nasihin ta da khas dinta da Aam din ta, kuma ya roki Allah Madaukaki ya bani fahimtar ta da hardace ta kuma ya sanya hannun sa a kan kirji na ya roki Allah ya cika zuciya ta da fahimta da kuma hukunci sannan sai ya gangaro da ruwayoyi wadanda a sarari suna kamanta abin da aka furta a wannan hadisin wadannan ruwayoyin sun hada da cewa akwai jafar da jami'a da mus'hafin fadima da ke wajen Ahlul-baiti ya kuma kawo sharhin ra'ayoyin Shi'a a cikin ma'anar samuwar wadannan litattafan a wajen Ahlul-baiti kuma ya fadi cewa: Lalle Shi'a sun ce imla'in Manzo ne kuma shiftar Ali kuma lalle babu wani na Kur'ani daga cikin ta kadai abin da ke ciki ya kunshi sharhi da labarai da fituntunu, sannan ya ambaci wasu ruawayoyin da suke yin nunn a kan cewa iamamai su ne masu ruwaito hadisi kuma su ne suke rike da wadannan ruwayoyin ta hanyar ruwayoyin Sunna daga ciki akwai fadinsa wanda Ahlus-sunna suka hadu a kan sa, daga ciki akwai fadinsa Manzo (s.a.w) "Lalla a cikin ku akwai masu ruwaito hadisi" da kuma fadinsashin sahabbai : Na kasance ina bada hadisi har sai da na gajiya" sannan bayan haka ya ciratu zuwa ruwaoyin da suke yin nuni a kan kadaitakar zurin halitta tsakanin Manzo da imamai, kamar irin fadin Manzo (s.a.w): Lalle Allah ya halicce ni sannan ya halicci Ali da Hasan da Husaini daga haske daya, sannan a karshen wannan fasali ya ce: To lalle mu kam a karshe zamu kai ga wata akida ta falsafa ko ta mitafizik a cikin lamarin imamancin da ta sa manzo da imamai suka zama jauhari guda daya na haske wanda ya gabaci halittar kasa, kuma a nan ne zamu isa zuwa nukda mihimmiya waccce zamu yi tambaya a kan ta, cewa mene ne matsayin imamanci kuma shin a mtsayi daya take da annabci ko kuwa, daga wannan ne zan kara korowa in ce: Lalle mutumnin da yake dauke da wannan a kidar ba a bin mamaki ba ne a sami faruwar wata akida kamar ta gullat da da'awar annanbtaka daga kurarta ba, kuma daga wannan za a iya samun wani sabon yanayi da wannan yanayin ya haifar. A nan maganar fargal ta kare a takaice tare da yin tasarrufi a ciki lafazin jimlolin nasa, bisa kiyaye abin da ta kunsa.
Ya bayyana a sarari daga karshen wannan fasali da muka rairayo cewa Faragal yana musanta wasu abubuwa kuma yana ganin su a matsayi wani nau'i na shisshigi wanda ita ce isma, sannan kadaitakar asali da zurin halitta tsakanin Annabi (s.a.w) da tsatsonsa (a.s), sannan kuma ya musanta abin da ake jingina wa Ahlul-baiti na daga ilimomi sannan kuma a karo na hudu kuma ya musanta matsayin imamai a bayan Manzo (s.a.w), na biyar kuma ya jingina wa Shi'a gullanci.

Rufewa
A nan zan fuskanci ustaz Faragal da tambaya ita ce: Da a ce duk wadannan abubuwan da ka musanta su ga Shi'a kuma suka zama akwai su a wajen Ahlus-sunna, shin su ma Ahlus-sunnar zai yi musu nakadi ne ko kuwa. Da sannu wannan tanbayar za ta baka mamaki, kuma harka ce ta yaya kuwa ba zai yi musu nakadi ba, alhali maudu'in daya ne kuma babu bambanci tsakanin kasantuwar Sunna ne suka fadi ko kuma Shi'a. A nan kuma zan baka amsa da cewa ba zai yi musu nakadi ba idan har suka zamo ba Shi'a ba ne, kuma wannan ne abin da ya faru a aikace, domin sun fadi wadannan abubuwan wadanda ya yi wa Shi'a nakadi a kan su, kuma da sannu zan dora hannun ka akan maganganun su a bayanai masu zuwa:
1- Lamari na farko: Abin da ya yi wa Shi'a nakadi da shi na isma, kuma ba na bukatar in maimaita abin da ya gabata na riga na fade shi, wanda kuma maganganu da yawa daga cikin malaman Sunna tuni suka yi nuni a kan sa dangane da isma, duk da cewa ba dukakkaninsu ba ne, amma tare da hakan Yahya Faragal bai musa ta hanyar yin nakadi ba, tare da cewa shi Yahya Faragal ya fi wanin sa sassauci a cikin wannan babin, saboda wasunsa sun fi shi tsanani da kuma kai farmaki, dauki misalign Dakta Nabih Hijab mamalmin adabi- ina ma a ce yana da adabin- na Darul ulum a Kahira, wannan mutumin yana zagin Shi'a zagi mai ban mamaki kuma yana ganin akidar su a kan isma alama ce daga cikin alamomin bangaranci, saurari abin da yake cewa:
Lalle wannan akidar daga Farisawa ta sudado zuwa cikin shi'anci wadanda sun kasance suna rayuwa a kan tsarkake sarki don haka ne ma larabawa suke kiran ta akidar da aka samo daga mulkin kisra- alhali ban san wani mutum guda da ya daga cikin larabawa da ya fadin wannan ba a iya bincike na, ta yiwu mafi yawan Shi'a an kasance ana jifan su da wannan a sakamakon akidar su ta tsarkake Ali (a.s) daga kuskure har ta'addancin Banu Umayya na kwace halifanci ya zamo ya fito fili, wannan ke nan. Kuma a cikin yahudanci akwai da yawa daga cikin mazhabobin da suka yi naso zuwa Shi'a.
Ka ji irin wannan shelar da na baya suke ta nakaltowa daga magabatan su bisa wauta, kuma tuni mun riga mun warware maka wannan tsammace- tsammacen a cikin abin da ya gabata na batun bafarisen shi'anci, sai dai abin da nake so in yi tambaya kan sa shi ne mene ne kuskure a cikin a cikin ayyukan Imam Ali (a.s) a mahangar Nabih Hijab, shin yakin da ya yi saboda kare tushen bubuwan da suke na dole, al'amarin da yya kai ga rashin samun tabbatacen yanayi na zaman lafiya, a daidai lokacin da yanayin Banu Umayya bai samu tabbatuwa ba sai a bisa cire wuyayen, koma dai meye, kuskurarwar Nabih Hijab ga Ali ba zai cutar da shi ba, bayan tuni Manzo (s.a.w) ya riga ya fadi cewa: Gaskiya tana tare da Ali kuma Ali yana tare da gaskiya. Kuma yana daga cikin abin da yake dabi'a ne a samu Ali tare da wadanda suke tare da shi da kuma Nabih Hijab da shi da wadanda suke tare da shi a daya bangaren.
2- Lamari na biyu: Abin da Faragal ya musanta wa Shi'a shi ne kasancewar Manzo (s.a.w) da ahlin gidansa daga haske daya suka fito, ban sani ba miye abin mamaki bayan Shi'a sun tabbatar da wannan daga masdarori ingantattu, shin ko dan wannan bai yi daidai da wasu san rai da suke cikin zukatan da ba sa bin Ahlul-baiti ba, ko kuwa? Sannan don me dan an sami irin wannan a wajen Ahlus-sunna ba ya zama abin mamaki, ga Zahabi ya ruwaito wani hadisi a cikin mizanil I'itidal, ta hanyar Abuhuraira daga Manzo (s.a.w) yana cewa: "Allah ya halicce ni da haske kuma ya halicci Abubakar da haske na kuma ya halicci Umar da hasken Abubakar kuma ya halicci Usman da hasken Umar, kuma Umar shi ne fitilar `yan aljanna , ban sani ba don me haske ya zo har kan Usman sannan ya ki karasawa kan Ali tare da cewa alal akalla shi ne halifa na hudu! Allah ne ya san girman lamarin ka ya Ali dan Abi Dalib!, ban sani ba mai Ustaz Faragal zai ce a kan wannan shin wannan gullanci ne ko kuwa?!, Ku zo mana da fatawa Allah ya gafarta malam, wannan ke nan. Tare da cewa dabi'a ne ya zama tsakanin mutum da ahlinsa akwai kadaitaka ta tsatso, alhali aalayen Muhammad (a.s) daidai suke da Kur'ani kuma taska ko kundin kuma ma'adanan ilimin Annabi ne su, to don me Ustaz Fafagal yake musanta musu abin da ba ya musanta wa wasunsu,
3- Lamari na uku: Abin da Ustaz Faragal ya musanta shi ne kasancewar ilimin Ahlul-baiti da shari'a da ilimomin Kur'ani da ilimomin Sunna madaukakiya kuma su zamo su ne masu bada hadisai, a nan za a iya cewa , lalle ilimin Ahlul-baiti ko da ya zama ta hanya ce ta al'ada kamar koyon ilimi ko zuwa makaranta, ko kuma ya zama ta hanyar ilhama da kuma cewa ana zantar da su hadisi ne, amma al'amari na daya, tabbatacce ne domin sun taso ne a gidan Muhammad (s.a.w) kuma an tarbiyantar da su a dakin sa sannan kuma sun karbi ilimomi daga wannan gidan kuma wannan lamari ne da babu wata kura a cikin ta, amma samun ilimi ta daya hanyar wato ta hanyar ilhama da kuma zantarwa kamar yadda wasu ruwayoyi suka yi nuni a kai. Musulmai baki dayan su sun tabbatar da wannan kuma da sannu zan ambaci wasu daga nassosinsu a cikin yiwuwar irin wannan ilimin:
Alusi ya na cewa a cikin tafsirin Ruhil ma'ani a yayin tafsirin ayar 65 daga surar Nahli: Shi ne fadinsa madaukaki: "Ka gaya musu ba wanda ya san abin da ke cikin sammai da kassai sai Allah" sai ya biyo bayan ta da cewa: Ta yiwu gaskiya shi ne a ce lalle ilimin gaibi da aka kore wa waninsa mai girma da buwaya shi ne wanda ya zamo da kan sa ma'ana ba da wasida ba wajen tabbatar da shi a gare shi, kuma abin da ya ke aukuwa ga kebantattun mutane baya daga cikin irin wannan da wani abu, kadai yana daga cikin wanda ya zo daga gare shi mahalicci mai girma da buwaya, yana mai kwararo baiwarsa gare su daga wata fuska daga fuskoki, ba za a ce sun san gaibu ba ta wannan ma'anar, domin lalle wannan kafircewa ne, abin da za a iya cewa anan shi ne sun bayyana ko sun yi tsankaye a kan gaibi .
Kuma abin da Alusi ya fadi, shi ne ainihin abin da ya zo daga Imaman Ahlul-baiti: Imam Ridha (a.s) na takwas daga cikin jerin Imamai yana cewa: "Yana yalwata mana ilimi sai mu sani kuma yana rike shi daga garemu sai mu zama ba mu sani ba" wannan ma'anar ita ce ainihin abin da wannan ayar take nufi: "Masanin gaibi baya bayyanar da gaibin sa ga wani sai dai wanda ya yardarwa na daga Manzo" aya ta 27/suratul Jinni. Dangane da sharhin wannan ayar ne Imam Ridha (a.s) yake cewa da Amru dan Hidab a lokacin da ya tambaye shi a kan ilimin Imamai, sai ya ce "Manzo Allah (s.a.w) shi ne yardajje a wajen Allah kuma mu ne magadan wannan Manzon wanda Allah ya tsinkayar da shi gaibin sa sai ya sanar da mu abin da ya kasance da abin da zai kasance har zuwa ranar ta shin alkiyama " a karkashin wannan ma'anar ne mafassarin nan Banaishabure ya ke cewa: Kore karama daga waliyai yana faruwa ne imma dai saboda Allah bai cencenci ya zama ahlin wannan ba, ko kuma saboda shi muminin ba ahlin wannan ba ne, kuma dukkanin wadannan korarru ne, domin dacen mumini da sanin sa, yana daga cikin mafi girman baiwar sa madaukaki ga bawan sa, idan har mai kwararowar bai yi rowar bada mafi girma da daukaka ba, hakan yana kasancewa ne saboda ba ya yin rowar bada abin da yake kasa de wannan.
Imam Sadik ya ba da haske a kan sashin ilimomin da suka ciro daga cikin Kur'anita hanya ta dabi'a, wannan ya faru ne a yayin da sashin sahabbabn sa suka tambaye shi, sai Imam Sadik ya ce: "Lalle na san abin da ke cikin sammai da kassai kuma na san abin da ke cikin aljanna da wuta kuma na san abin da ya kasance da abin da zai kasance" yayin da mai tambayar ya yi mamakin maganar sa sai Imam ya ce : "Na san wannan ne daga littafin Allah mai girma da daukaka wanda yake cewa: "Mun saukar maka da littafi yana mai bayyanawa ga komai domin shiryarwa da rahama da kuma bushara ga muninai" 89/ daga surar Nahal. Kuma lalle an ruwaito daga gare shi da kuma nazariyyar yiwuwar Ahlul-baiti su sha ililmi dan kadan ta mahanga faffada .

Sunna Da Ilimin Gaibi
Bayan da muka riga muka yi nuni a kan zuwa cewa lalle Shi'a Imamin da yake da cikakken tanadin da Allah madaukaki zai kwararo masa daga hasken sa da ilimin sa saboda idan har aka samu wanda zai iya karba to babu rowa a cikin falalarsa madaukaki, saboda haka ilimin gaibi shi a kan kan sa a ra'ayin Shi'a na Allah ne madaukaki, amma ilimin Ahlul-baiti ko dai ya zamo kwararowa ce ta kai tsaye daga wajen Allah Madaukaki ta hanyar ilhama ko kuma zantarwa ko kuma ta wasidar Annabi, haka ne ba ma musanta samuwar wadanda su ke yin guluwi a kan Ahlul-baiti, amma mukam mun barranta daga wadannan, kuma da sannu zamu shude zuwa wannan sai dai abin da nake so nace shi ne: Lalle Ahlus-sunna suna tabbatar wa shuwagabannin su sanin gaibi kamar yadda `yan'shia suke yi kuma suna ganin ana zantar da su, daga cikin irin wadannan misalsalin, akwai abin da Dabari ya ruwaito a cikin tafsirin sa ga aya ta 25 daga sura haj.
"Kuma ba mu aiko wani Manzo ko Annabi gabanin ka ba…" zuwa karshen ayar. Sai ya ce ya zo daga Ibn Abbas cewa ya kasance yana karata ayar kamar haka ko Annabi ko mai zantarwa. Muslimata dan Kasim dan Abdullah ne ya ambance shi kuma Safiyanu dan Umar dan Dinar ya ruwaito shi daga Ibn Abbas, Muslimata ya ce: Sai muka samu masu ba da hadisi a rike suke kam da annanbta domin sun yi magana akan abubuwa madaukaka fiye da labarin gaibi, kuma sun yi furici da boyayyar hikima kuma suka zama sun dace a cikin abin da suka fadi kuma aka kare su a cikin abin da suka fadi kamar misalin Umar dan Khaddabi a cikin kissar mayaka da kuma abin da ya yi furuci da shi na wanda yake hujja ce madaukakiya. Wannan shi ne abin da Kurdabi ya ruwaito shi , Siyudi ma ya ruwaito wannan kira'ar da aka ambata kuma ya yi magana akan masu zantarwa a cikin tafsirin Durrul Mansur, ka koma can .
Buhari ya ruwaito a cikin littafinsa babin darajojin Umar, ya ce: Manzo (s.a.w) ya ce: Lalla akwai a gabanin ku na daga Banu isr'ila wasu mazaje suna yin magana ba tare da sun zamo annanbawa ba, kuma idan har akwai makamancinsu a cikin al'ummata to Umar ne, kamar yadda muslim ya fitar da shi a cikin sahihinsa a cikin babin falalar Umar daga A'isha daga Manzo (s.a.w) lalle ya kasance akwai wadanda ake yi wa ilhama a gabaninku idan kuwa akwai wani daga cikinsu a cikin al'ummata, to Umar ne .
Kuma lamarin bai tsaya a kan shuwagabanni ba ya kai har ya kai ga Imrana dan Husain, daga Mudrif ya ce: Imrana dan Husain ya ce da ni: Ashe ba na zantar da kai wani hadisi ba ko Allah ya amfanar da kai da shi, lalle Manzo ya hada tsakanin hajji da umra kuma har ya rasu bai hana ba, kuma Kur'ani bai sauka yana mai haramtawa ba, na kasance ina ba da habisi har sai da na gajiya sai na daina, sai kuma na daina kasawa, sai hadisin ya dawo. Haka nan kowanne daga cikin Darumi da Muslim duk sun ruwaito wannan hadisin a sahihansu .
Ban sani ba mene ne alakar kasa magana da guduwar hadisin? Sanin wannan yana wajen Husain, Allah ya rahamshe shi.
Balllantana ma abin da suka ce na Umar dan Abdul'aziz halifan Umawayya cewa Hidhir ya kasance yana tafiya tare da shi, kuma yana zance da shi kamar yadda Ibn Hajar ya ruwaito a Tahzib .
Bayan dukkanin wadannan abubuwan da muka fadi shin zai sa ya zama Ahlul-baiti su zama suma suna daga cikin wadanada ake kwararo musu ilimi ko kuwa? Mafi rinjayen zato shi ne har yanzu ishkalin ba zai gushe ba yana nan, kuma lalle dai Shi'a sune gullawa ko kuma masu cenja addini saboda suna cewa Imamai sun san gaibi.
Na hudu: Abin da Ustaz Faragal ya musanta na matsayin Imaman Ahlul-baiti ya zamo ya biyo bayan matsayin Manzo (s.a.w) kai tsaye a wajen Shi'a, kuma wadanda da ake nufi su ne Imamai goma sha biyu kawai banda wasun su, kuma Shi'a ba su ne suka ajiye imamai a wannan matsayin ba, su Shi'a sun bi umarnin sama ne a matsayin su na bayi, Allah Madaukaki yana cewa: "Kadai shugaban ku shi ne Allah da Manzonsa da kuma wadanda suka yi imani wadannan da su ke tsaida salla kuma suke ba da zakka alhali suna cikin ruku'u". 56: Ma'idah. Ruwayoyi sun zo da yawa a kan cewa ta sauka ne a kan Imam Ali kuma ta sanya shi abokin tarayya a cikin shugabanci, kuma kowanne daga Fahrurraz a cikin tafsirin sa da Ibn Jarir Dabari, sun ruwaito wannan a cikin littafinsu, haka ma Baidhawi a cikin tafsirin sa da Ibn hayyan a cikin tafsirin sa da kuma Zamakhshari a cikin tafsirin sa da Ibn kasir a cikin tafsirin sa da kuma makamancin su, sannan bayan Kur'ani mai girma Sunnar Annabi ta ba shi wannan matsayin. Manzo (s.a.w) yana cewa: "Kai a wajena kamar Haruna na a wajen musa sai dai cewa babu Annabi bayana, kuma wannan hadisin yana daga cikin hadisai mutawatirai, kuma ma'abota sahihai sun fitar da shi, daga cikin su akwai Buhari da Muslim da a cikin ingantattun su a cikin babin falalolin Ali na sahih Buhari haka ma a Sahih Muslim.
`Ya`yan Ali ne su ke bin sa a bayan sa, kuma Annabi (s.a.w) ne ya sanya su a wannan matsayin, kuma babu wani abu da yake yin nuni a kan haka sama da sanya su da ya yi a matsayin tagwarorin Kur'ani, a inda yake cewa: Na bar muku masu daraja guda biyu littafin Allah da kuma `ya`yan gida na mutakar kun yi riko da su ba za ku taba bacewa a baya na ba har abada..h.k. , yanzu kuma mu koma zuwa tunani irin na Sunna; zamu samu cewa yana ajiye Imaman sa a irin ainihin wannan matsayin ba tare da musantawa ba, balle ma mahangar ta su tana ganin cewa Annabi (s.a.w) wanda shi da wahayi ake saita shi da zai wadatu daga bukatuwa ba daga wadannan Imaman. Hakim yana fadi a cikin mustadrak da sanadi zuwa Huzaifatu binil Yamani: Na ji Manzo (s.a.w) ya na cewa: "Hakika na himmantu da aika mutane zuwa sasanni su rika koyar da mutane sunnoni da farillai kamar yadda isa dan Maryam ya tura Hawariyyun, sai aka ce da shi to mai ya hana ka tura Ababakar da Umar sai ya ce: Ban wadatu daga gare su ba a cikin addini domin su kamar ji ne da gani . Balle ma Sunna sun ba wa sahabbai matsayin da ya yi daidai da matsayin Annabi ta bangaren kasantuwar zancensu da ayyukansu hujja ne da sanya su matsayin madogarar shari'a. Musa Jarullah yana fadi a cikin Washi'a "Mu ne fakihan Ahlus-sunna wal Jama'a muna sanya sunnar shaikhunnai guda biyu (Abubakar da Umar) a matsayin tushen wanda ya yi daidai da sunnonin mai shari'a annabin rahama wajen tabbatar da hukuncin shari'a cikin rayuwar al'umma da gudanar da daula, kuma lalle halifanci ne shiryayye ma'asumi irin ma'asumancin Manzanci, mai nagarta da zai tabbatar da rukunan addinin Musulumci ". Kaga halifofi kamar yadda Jarullah yake kawo nassi akan su a nan abubuwa ne da suka yi daidai da sunnar Annabi da kuma nassin Kur'ani, kuma halifofi ma'asumai ne kamar dai Annabi (s.a.w) kuma lalle sun yi rabebeniya da Annabi, (s.a.w) su suke rike da rabin hukunce-hukuncen da aka kafa Musulumci a kan su, Annabi (s.a.w) kuma yana dauke da kaso na biyu, kuma Imam gazali yana cewa: Mazhabar Sahabi daya hujja ce kai tsaya .
Kuma Ibn Kayyim Jauziyya yana cewa: Lalle fatawoyin sahabbai su suka fi cencenta da a yi riko da su ko da kuwa sun yi sabani idan kuma halifofi hudu suka kasance a wani bangare to babu makawa shi ne daidai, idan kuma mafi yawan su suka kasance a wani bangare to abin da yake daidai yana tare da mafiya rinjaye daga cikin su, idan kuma suka zamo mutum biyu- biyu, to bangaren da Umar da Abubakar suke shi yafi kusa da daidai, idan kuma Abubakar da Umar suka saba to gaskiya tana tare da Abubakar, don lokacin da ya fi kusa da na Manzo to shi ya fi kusa da daidai . Ban san me dan Taimiyya yake nufi da kusancin zamani da na Manzo ba, idan har ya kasance yana nufin kusanci na zamani to dukkaninsu sun kasance a zamani daya tare da Annabi (s.a.w) idan kuma yana nufin kusanci na wajen zama kari a kan abin da ya gabata to Imam Ali shi ya fi lazimtar Annabi fiye da inuwarsa, saboda haka bisa dalilin Ibn Taimiyya ya wajaba a gabatar da maganarsa idan ta ci karo da maganar waninsa.
Bari in ba ka labarin abin da yafi wadannan dadin ji baki daya: Maganar sashin malaman Ahlus-sunna ta zama ma'auni wajen gyara Kur'ani da hadisan Annabi (s.a.w) idan Kur'ani da Sunna suka sabo da fadin wannan imamin: Karkhi daga cikin Imaman hanafiyyawa yana cewa:
Asali shi ne wajabcin yin aiki da maganar Abuhanifa, idan ya dace da fadin Kur'ani da Sunna to shi ke nan idan kuma ba haka ba, to ya wajaba a yi tawilin Kur'ani da Sunna daidai da fadin Abuhanifa. Ustaz Rashid Ridha ya ambaci wannan a ciki tafsirul manar a yayin da yake fassara ayar: "Akwai daga cikin mutane wadanda suke rikar wasu kishiyoyi ba Allah ba" aya ta 165/ Bakara . Sai kuma ga Kushaji shi ma yazo da kwatankwacinta, idan har shi Karkhi ya sanya fikihu hanafiya ma'aunin da za a riga gwada littafi da Sunna da shi, to shi kuma Kushaji halifa Umar ya ba wa hakkin yin ijtihadi alhalin ga maganar Annabi! Ka saurare shi a cikin bahasinsa a kan Imamanci a cikin littafin Sharhin Tajrid a inda yake cewa: Lalle Umar a yayin da yake kan mimbari ya ce: Ya ku mutane abubuwa uku sun kasance a lokacin Manzo kuma lalle na yi hani a kan su kuma ina haramta su sannan kuma zan yi ukuba a kan su, mutu'ar mata da mutuar hajji da kuma hayya ala khairul amal. Sannan Kushaji ya ci gaba da cewa: Lalle wannan bayanin na daga cikin abin da za a yi suka a kansa, sabawa mujtahidi ga waninsa a cikin mas'alolin na rassa ba bidi'a ba ne .
Bayan wannan kuma sai muce da ustaz Faragal: Muna sanya imamanci bayan annabci kuma muna daukar wannan a matsayin abin da Allah ya saukar ne cewa; Allah ya bawa Imami irin cancantar da ya ba wa Annabi, amma dai mu ba ma daukar Imami a matsayin ma'aunin da za a rika auna Kur'ani da Sunnan da maganganunsa, mu mun tafi a kan akasin hakan. Ma'auni shi ne Kur'ani da Sunna, kuma duk abin da ya saba musu nana shi muke da bango, kamar yadda ba ma halarta yin ijtihadi alhali ga Kur'ani a gefe, kamar yadda Kushaji yake ganin Manzo a matsayin wanda yake yin ijtihadi, kuma lalle wannan ya saba da fadinsa madaukaki: "Baya yin furuci da son zuciya face sai in wahayi aka yi masa" ayoyi na 3.4/ Najmi. Duk da haka kimantawa da ba wa Imamai matsayi da muka yi abin mamaki ne a wajensu, a yayin da wasunmu kuma da bakunansu suke ba wa Imamansu matsayin da muka ambata, tare da haka ba a samu wanda zai yi musu nakadi ba, ya a ka yi haka ta faru ya kai Ustaz Faragal? Shin kuwa ka taba yin wata hobbasa kai da makamancinka domin ku tambayi kanku a kan ingancin akidojinku ko kuma ku yi musu nakadi kamar yadda kuke yi wa wasunku? ko kuma ku ne matanen Allah zababbu wadanda ya halatta a gare ku abin da bai halatta ga wasunku ba.

5- Lamari Na Biyar:
Ustaz Faragal yana ganin cewa ruwaoyin Shi'a suna tatter da yanayin da ya dace da samuwar gullawa, a nan ina so in yi wa Ustaz Fragal sharhi a kan matsayin Shi'a daga gullanci da kuma gullawa: Dabrasi ya yi ta'arifin gullanci a cikin tafsirin sa a yayin da yake yin sharhin aya ta 77/ Ma'ida: "Ka ce ya ku ma'abota littafi kada ku yi shisshigi a cikin addinin ku ba bisa gaskiya ba" da cewa shi ne abin da yake kishiyantar takaitawa, kuma shi a ke kira wuce iyaka, sai ya ce ai "Ana nufin kada ku wuce iyakar da Allah ya ajiye ku a kan ta har ku zama kun wuce iyaka kuma kishiyar wannan shi ne takaitawa, takaitawa kuma ita ce fita daga iyaka zuwa tauyewa, kuma ka ga yin sama da abin da ya kamata da kuma yin kasa da shi dukkanin su barna ne, kuma addinin mu wanda Allah ya umarce mu da shi yana tsakanin wuce iyaka da kuma takaitawa wannan ake kira tattali ko tsakaitawa- .
Amma dalilan da ke jawo wuce iyaka mafi bayyanar su kuma mafiya mihimmanci daga cikin su a mahangar mu dalilai ne duga hudu kamar haka:
A- Mafara (Sababi) ta farko:
Idam mutum ya wuce iyaka a kan wani mutum ko wani tunani, domin ya riki wannan a matsayin dallilin da yasa shi ya riki wannan tunanin ko kuma muutmin, domin yana so ya yi riko da abin da zai zame masa kariya a gaban mutane kuma abinada zai zama gamsarwa a gare shi, ya kuma ta yin kokarin zuzzuta wannan tunanin, sosan gaske bisa akidantuwarsa da wannan mutumin, domin su mabiya a ko da yaushe suna yin kokarin daukaka matsayin wanda suke yin koyi da shi zuwa wani matsayi da ya wuce na dabi'a, kuma wannan ma'anar samammiya ce a fagen addini da na siyasa, an siffanta Sarki Hubar da cewa mutum ne da yake fassara iradar Allah da kuma ta mutane, ta yadda ya bashi iko mudlaki a wajen yin tasarrufi kuma bai ba wa mutane damar cire shi ba, shi ya sa ma ake ganin iradar sa a matsayin irada ce daga Allah madaukaki.
Malaman falsafa na Yunan sun tafi a kan wannan ra'ayin bisa la'akari da tasirin da suka tabbatarwa sarki na daga siffofi, wanda ya fisu tsananna tawa a cikin wannan shi ne, Haijal malamin Markis, a wajen sa sarki shi ne ma'abocin sarauta mudlaka kuma yana da cikakkiyar dama a kan maslahohin daidaikun mutane kuma mutumtakar sa na misalta zati na karshe wato shi ne dunkulen tarayyar al'mma a cikin mutum guda, shi ne shi ne.. kuma tuni afladul ya rigayi wadannan baki daya a yayin da ya bawa sarki tsarkakakkun matsayoyi, haka ma Farabi a ya yin da suranta sarkin gari da cewa a hade ya ke da hankali mai tasiri ta yadda yake kasancewa kusa da Allah Madaukaki .
Lalle wadannan matakan matakai ne bawa kai hanzari a kan yin riko da wani tunani bisa wani yanayi ko kuma da wani yanayin na daban da zai iya kaiwa da a yi wani ko a yi riko da wani tunani na musamman.
B- Abu na Biyu da ke sa a yi Shisshigi:
Sakamakon Takura: Akan azabtar da wasu saboda a kidunsu, ta yiwu a aibata shi ko a zage shi ko a yi masa izgili ko sai wannan ya sa shi ya wuce iyaka saboda sakamakon dabi'ar kome ta turi in tura, saboda haka ne ma muka ga Kur'ani mai girma irin wadannan wajajen ya yi riko da dabi'a ta rai da zuciyar dan Adam tare da ba wa wannan lamarin cikakkiyar kulawa a yayin da madaukaki yake cewa: "Kada ku zagi wadanda su ke bautawa ba Allah ba, sai su zagi Allah saboda gaba bisa rashin sani"108/ Na'am. Kuma wannan masa'alar tana da tabbatattun gwaje- gwaje a tsawon tarihi a wurare da dama daga wannan ne ma Donaldus ya tafi a kan cewa: Lalle ra'ayin isma sakamako na takurawar da halifofin da suka yi kwacen mulki suka haifar da shi, kamar yadda yake tsammani.
Kai bangon takurawa ta taka rawa mai girma a tarihin Musulmai da akidunsu kuma ya zama wajibi a yi riko da wannan sosai a yayin da za a yi kokarin daidaita matakai da kuma saita nassosi a wurare da dama.

C- Mafara Ta Uku:
Shin gullatancin da yake faruwa sakamakon tsarkaka da kuma barranta da kyautata zato ga wasu sai aka jingina shi zuwa abin da suka ruwaito ba tare da tantance wa ba musamman ma ga wadanda suke yi wa Musulumci dasisa saboda wannan dalilin ko wancan kuma suka yi kokarin lullube hakikanin su sai suka yi hamasa hamasar da ke iya haifar da shubuha ga wasu mutane ko ga tunani, wannan mafarar magana a kanta na da tsawon gaske. Da yawa daga cikin masu yin dasisa sun taka rawa ta sarari domin su sajjala tunanin da kuma matakai wadanda su ke kaiwa ga wuce iyaka har ta kai ga suka bata wa Musulmai da yawa akidun su saboda manufofi mabambanta wadanda su ne su ka zuga su, kuma lalle kowace mazhaba daga cikin mazhabobi suna da wani kaso na wadannan ko kuma kaga sun karanta saboda yanayin mazhabar ita a kan kan ta kuma ta yiwu wannan ma'anar (lamarin) ta shude da mu a nan gaba dalla-dalla.
A. Dalili Na Hudu:
Ta yiwu a jarrabi wasunsu da shubuhar da za ta kai su zuwa ga sakamako kuskurarriyar fahimta ko kuma yin gamemmen hukuncin da ba a warware shi ba a ilimance kamar idan ya ga wani ra'ayi na wani mutum daga cikin wata mazhaba sai ra'ayin sa ya game dukkanin yan mazhabar gaba daya, kuma ta yiwu wasu jama'a su tafi a kan wani ra'ayi sannan kuma jama'ar su kare, sai kuma ka ga wani ya zo ya dorawa wasu ra'ayin, kuma ta yiwu fitar da wani sakamako a kan wani ra'ayi ya zama ya lazimci tafiya a kan wani ra'ayi wanda shi kan sa mai wannan ra'ayin bai fahimci hakan ba, kuma ta yiwu ya zama ya faru ne sakamakon yin kuskure a wajen dabbaka wata ka'ida gammamiya a kan wasu sasanni da makamancin wannan, babu makawa da a rika bi sannu- sannu kuma rika kiyayewa da gaske ta yayin rubutu a kan wasu matane ko kuma mazhaba, babu makawa da a riki ra'ayin ta daga masdaran ta wadanda aka yarda da su kuma aka sallama musu, idan sashin Shi'a a wani lokaci suka kasance sun wuce iyaka akan Imam Ali saboda ya cizge kofar khaibar, ba dukkanin Shi'a ne suke hake ba, idan har wani mutum ya ce da Imam Ali a lokacin da ya ke yin huduba sannan ya ce da shi kai ne! Wannan ba yana nufin dukkanin Shi'a haka su ke ba.

Matsayinmu A Kan Shisshigi Da Wuce Gona Da Iri
Bayan sharhin abubuwan da suka haifar da guluwwi, da kuma mihimmai daga cikin su, zamu iya cewa lalle Shi'a saboda biyayyar su ga Imaman su sun tsaya a matsaya ta tsaftacciya daga gullanci da gullawa sai su ka fito da su sarari kuma suka barranta daga gare su kuma suka yake su kuma suka zare takobi a gabansu, kuma su da wannan matsayin da su ke kai ba za su ketare matsayin amirul muminin (a.s) ba, a yayin da yake cewa "Mutum biyu sun hallaka a kai na mai yi min son da wuce iya ka da kuma mai ki da ya tsananta gaba". Imam Sadik ma a yayin matsayin sa, a yayin da yake cewa: "Mu ba kowa ba ne face sai bayin wanda ya yi halitta kuma ya zabe mu, na rantse da Allah ba muda hujja a kan Allah kuma wallahi ba mu da wata makubuta daga Allah, kuma lalle mu masu mutuwa ne kuma ababan tsayarwa ne kuma ababan tambaya ne, wanda ya so masu wuce iyaka (gullat ko gullawwa) ya ki mu, wanda kuma ya ki su hakika ya so mu, gullat kafirai ne, mufawwidha kuma mushirikai ne Allah ya la'anci gullat, ku saurara, su sun zamo nasara, sun zamo kadariyawa, su murji'awa ne kuma hururiyyawa".
Kuma Imamiyyawa ba sa gadar da gullat (ba su halatta aba su gado ba) kuma ga yadda nasiin maganganun su yake, ma'abocin hakki daga cikin musulmi yana yin gado tsakanin mabarnaci daga cikin su, da wanda yake mabarnaci haka ma tsakanin wanda yake kan gaskiya da kuma wanda yake mabarnaci, in banda gullat, Musulmai za su gada daga gare su su kuma ba za su gada daga Musulmai ba, kamar yadda imamiyyawa ba sa wanke gawar gullat kuma ba sa binne su, sannan kuma sun haramta a aura musu, da kuma ba su zakka, kuma zaka sami wadannan hukunce- hukuncen a ko ina a tsakaknin litattafan fikihun imamiyya a cikin babobin tsarki da zakka da gado, kuma lalle imamiyya ba sa sanya gullat a matsayin Musulmai:
Shahidai guda biyu na farko da na biyu suna fadi a cikin Lum'atul dimashkiyya¸ a cikin babin wakafi a yayin da yake yin ta'arifin musulmi: Musulmai su ne wadanda suke yin salla suna masu kallon al'kibla ai wanda ya akidantu da yin salla zuwa gare ta koda kuwa bai yi sallar ba ba tare da yana mai kore hakan ba, in ban da hawarijawa da gullat wadanda ba a sa su a cikin jerin Musulmai ko da kuwa sun yi salla suna masu kallon al'kibla saboda an yi hukunci aka kafirtar su, kuma masu bawa Allah kama da siffa (mushabbiha) ma ana sasu a cikin su, su da masu yi wa ko tabbatar wa Allah jiki, balle ma Imam Sadik yana ganin zama da gullat da kuma gasgata zancen da yake fadi na jawo mutun ya fita daga imani, kamar yadda Fadhal dan Ziyad ya ruwaito yana cewa: Baban Abdullah Assadik ya ce a yayin da aka ambaci sahabban Abil Khaddab: " Kada ku zauna tare da su kada ku ci tare da su kuma kada ku sha tare da su kuma kada ku yi hannu da su sannan kada ku gadar da su" kuma Imam Sadik ya ce wa Marazim -daya daga cikin sahabban sa "Ka gaya wa gullat ku tuba zuwa Allah domin ku fasikai ne mushirikai".
?
Ra'ayin Sashin Masu Bincike
Daga wannan ne shehul Mufid ya ke cewa: Gullawa suna daga cikin masu bayyana Musulumci kuma su ne wadanda suka jingina wa shugaban muminai Ali dan Abi Dalib da zuriyar sa allantaka da annabta kuma suka siffanta su da matsayin da ya wuce iyaka a cikin addini kuma suka wuce iyaka don haka su kafirai ne".
Ba ina son in cika ku da nassosi a kan kubutar Shi'a daga gullanci ba ne, amma wane matsayi ne ya fi zama a sarari fiye da wadannan matakan da na ambata. A she bai isar wa munini ya zamo ya yi imani da Allah da kuma Manzonsa ya kuma yi riko da koyarwar Musulumci a cikin ayyukansa ba, har sai ya kai ga yin guluwwi a cikin wata akida ko kuma ga wani mutum, sai dai in wanda Allah ya shafe masa basira ba ne shi. Kuma saboda yadda matsayin Shi'a ya ke a sarari a kan gullawa ne ya sa mutanen da suka san abin da suke, su ke bayyana barrantar su gada gare su, daga cikin masu shelanta hakan akwai mawallafan Da'iratu Ma'ariful Islamiyya, ya zo a cikin Da'iratu Ma'arif cewa:
Zaidiyya da imamiyya su ne wadanda su ka yi riko da mazhabar tsakiya kuma suna yakar hululiyyin yaka mai tsanani kuma hululiyyun ba ma sa su a cikin Shi'a kamar yadda ya gabata kuma suna ganin su a matsayin gullawa wadanda suke bata mazhabar ,kai suna ma ganin su a matsayin wadanda suka fita daga cikin Musulumci.
Kuma Dakta Ahmad Mahmud a cikin Nazariyatul Imamiyya a yayin da ya bijiro a kan Mazhabar Babiya da Baha'iyya: A cikin bayabiyya akwai ra'ayoyi wadanda suka wuce iyaka wadanda suka sa ta zama mazahabar da ta ke wajen Musulumci dari bisa dari, kuma malaman Azhar a Misra da malaman Shi'a a Iraki da Iran sun hadu a kan kafircin Babiyya da Baha'iyya, sannan aka rife wajen haduwar Baha'iyya a Misra . Kuma Dakta Ahmad Amin ya bijiro da magana a kan motsin gullkawa, sannan ya ce: Lalle wasu daidaikun wawaye ne (basidai) wadanda suke allantar da Ali kuma lalle Shi'a sun barranta daga gare su, kuma a wajen su bai halattaba a yi musu salla. Wadannan kananan misalsali ne a kan lamarin gullanci da kuma gullawa da na ajiyye su a gaban wadanda suka saba da jifan Shi'a da wace iyaka, ba kuma ina kore yiwuwar sunan ya hau kan su ba da nufin cewa sun jingina kansu da mutanen da suke fifita Ali ko suke kiran kansu da Shi'a da yanayi na wuce iya ka ba, wadanda suka riga suka jingina masa wasu maganganu da ra'ayoyi da suke tattare daukaka, alhali tuni an yi wadannan mutanen an gama dasu da ra'ayoyin su baki daya, babu sauran irin su a yanzu sai a cikin litattafai, kuma yana daga cikin irin wannan abin da Bagdadi ya ruwaito, a cikin A lfirak bainal firak, a inda yake cewa: Imamaiya su na daga cikin Rafidhawa kuma sun kasu zuwa kaso goma sha biyar, sun e: Kamaliyya da Muhammadiyya da Bakiriyya da Nawusiyya da Shamdiya da Imariyya da Isma'iliyya da Mubarikiyya da Musawiyya da Kadiyya da Isna ashariyya da Hishamiyya da Zarariyya da Yunusiyya da kuma Shaidaniyya. Domin mukamala maganar Bagdadi sai mu ce: Imamiyya su ne Isna ashariyya kuma sune jamhurun Shi'a a yau kama babu samuwa ga wasun su a yau in banda Zaidiyya da kuma Isma'iliyya a wannan zamanin. Sannan Isna ashariyyan wadanda su ne bugiren binciken mu sun fifice wasun su da akidun su, kuma bai halatta a jingina musu ra'ayiyin wasun su ba, domin su ne kawai wadamda suna da kuma wasu abubuwa suka hada su da su, wani abu kuma shi ne wadanda Bagdadi ya ambata ta yiwu ya zama kowace firka bai yan wasu mutane yan kadan take da su ba wadanda su suke misalta ta. Wannan irin kwashi kwaraf da kuma sakaci wajen tantancewa mun dade muna ganin irin sa a cikin litattafan mazhabobi, na su Ibn Dahir da wasun sa, dauki misalign abin da Ibn Dahir ya ke fadi a cikin littafinsa Alfirak bainal firak an karbo daga Jabir dan Yazidul Ja'afi yana cewa:
Jabir dan Yazidul Ja'afi yana daga cikin Muhammadiyya, su ne sahabban Muhammad dan Abdullahi dan Hasan, sana sauraren bayyanar sa, kuma ya kasance yana tabbatar da (raj'a) (dawowa) dunuya bayan mutuwa kafin ranar alkiuyama.
Jabir baya daga cikin mabiyan Muhammad dan Abdullahi dan Hasan ba kuma bai kasance wanda ya tafi a kan raj'ar matattu kai tsaye ba, kadai abin da ya ke fadi shi ne raj'ar sashin wasu daga cikin Imaman Ahlul-baiti saboda ruwayoyin da ya ji, ba wani abu sama da hakan. To ka ga yadda tahkiki ya ke a wajen irin su Dahir marubuta kai ka ce lamarin akida abu ne mai sauki kamar haka, ta yadda zai rika jinginawa mutane abin da ba su fadi ba kuma ya sa su a cikin wasu mutanen da ba sa daga cikin su.
Bari in dawo kan lamarin gullat, tuni matsayin Shi'a a kan gullat ya riga ya bayyana ga mai karatu a sarai, amma tare da haka sai ka samu mai bincike kamar Zubaidi ma'abocin littafin Tajul arus, yana yin ta'arifin Imamaiyya a cikin littafin na sa da cewa: Imamiyya wasu bangare ne na gullatun Shi'a , sai ga Dakta Mahmud Hilmi a ciin littafinsa Tadwirul Mujtama'il Islamil Arabi yana cewa: An kira su da Shi'a saboda sun bi Ali kuma sun fifita shi a kan sauran sahabban Manzo (s.a.w) kuma yan Shi'a sun kafa dalilai da nasossi na Kur'ani wadanda suka fassara su bisa nazarin su kuma wasu daga cikin Shi'a sun wace iyaka a wajen tabbatar da cancantar Ali dan Abidalib kuma suka rubanya masa da sashin suffofin na tsarkaka da kuma allantaka , lalle zaka yi mamakin furucin wadannan marubutan, musamman sashin marubutan misra, domin su suna suranta Shi'a kamar wasu mutane ne da ba su da imani da addini, suna wasa da nassosi ba tare da mai bin diddigi daga Allah Madaukaki ba kuma ba tare da wasu ka'idoji na ilimi ba, na rantse da Allah su suka fi kusa da wannan, in ba haka ba meye dalili a kan abin da Mahmud Hilmi ya fada? Alhali ga littafain Shi'a nan a gaban sa, ya nuna mana wajen da Shi'a suka jingina hululiyya da allantaka ga Ali, kuma tabbas yanke ba zai sami wannan ba, sun kasance suna fitarda abin da suke fadi ba tare da jin cewa akwai wani nauyi a kan su ba: "Kalma ta girmama wacce take fita daga bakunan su, ba komai suke fadi ba sai karaya" kahafi/5. A bin da yafi wannan zama bala'i shi ne samun wadanda suke tasirantuwa da wadannan marubutan daga na kusa da su ko wanda ya ke nesa da su alhali kama shi dan Shi'a ne kuma kaga shi ma yana yin rubutu da irin wannan salon, Allah ya jikan wanda yake cewa:
Zaluncin makusanta ya fi tsananin daci*
*Ga mutum fiye da sara da takobin hindu
Dakta Kamil Musdafi yana fadi a cikin littafinsa: Bisa wannan ne zai a bayyane cewa lalle gullawa ko da kuwa sun kasance wadanda Shi'a da Imamansu, suke kin su, to tuni dai sun riga sun assasa akidun Shi'a na asali tun farkon farawa, kuma isma da ilimi na daga Allah sun zama tabbatattun rubutattun akidun Shi'a daga baya sai dai bisa sassauka yanayi, wannan ke nan, sai ta bayyana a gare ni cewa Dakta Kamil ya Dauki wannan ne daga Dakta Tasrihi dan Naufi, kuma shi dan daya ne daga cikin sahabban mukhtar, bari kuma in kara tuna mana da cewa lalle Shi'a sun riki akidun su ne daga Kur'ani da Sunna kamar yadda muka kafa dalili a kan sa a cen baya. Sannan da zamu kaddara cewa dan Naufi din nan ko kuma mukhtar sun riga sun fadi wata magana wacce ta shafe su, to mene ne lefin Shi'a? Kuma shi dan Naufal din shi waye har da zai taka rawa da sunan Shi'a? Idan har Dakta Kamil ya yi i'itirafi da cewa Shi'a da Imaman su ba sa son gullawa to ta yaya kuma Shi'a zasu karba daga gare su alhali saboda wuce iyaka su ka yi fushi da su? Idan kuma har wadannan akidun sun kasance daga cikin gullanci kuma shi baya yin sa a she wannan bai zama zunzurutu tanakudhi (maganganu guda biyu su ci karo da juna) ba?. Idan har mun kasance muna yi wa Hilmi da makamancin sa uzuri saboda ba su rike mu masdaran mu ba, to mene ne uzurin irin su Kamil Sha'abi wanda ya ke daga cikin Shi'a kuma yana rayuwa tare da masdarorin su, ba wannan ne kadai abin da Dakta Kamil ya fitar ba wanda ba mu yarda da shi ba, balle ma yana da wasu abubuwan da ya rubuta masu yawa irin su daga ciki akwai: Yayin da ya bijiro da masdarori a kan lamarin raj'a a wajen Shi'a ya fadi cewa asalin ta wasu kalmomi ne na Imam Ali (a.s) wadanada suka zo a cikin nahjul balaga yayin da Allah ya bashi nasara a kan mutanen jamal (rakumi) (a yakin jamal) a lokacin da sashin sahabban sa suka ce da shi na so a ce lalle dan'uwan wane ya halarci mu domin ya ga yadda Allah ya baka nasara a kan makiyan ka, sai Imam Ali (a.s) ya ce shin zuciyar dan'uwan ka yana tare da mu? Sai ya ce na'am, sai ya ce ya halarce mu.
Ta yiwu ya zama Imam yana yin nuni ne zuwa ayar nan "Kada ku yi tsammanin cewa wadanda a ka kashe a cikin tafarkin Allah matattu ne, balle ma rayayyu ne a wajen ubangijin su ana azurta su"Ali imrana/169. Alhali labarin yana komawa ne zuwa aj'a tare da dukkanin abin da ke cikin ta na daga ma'ana mai zurfi, balle ma sauran labarin yana kutsawa zuwa wani fage mafi zurfin ma'ana da falsafar raja'a da kuma hikimar ta, domin Imam yana cewa:
Wasu mutane daga cikin tsatson wasu mazaje da mahaifar wasu mataye sun halarce mu a cikin rundunarmu wannan kuma da sannu zamani zai rayu da su kuma imani ya karfafa da su, daga wannan, ya bayyana cewa lalle Ali a nan ba kawai ya tabbatar da dawowar wadanda suke gabata ba ne a cikin wannan jihadin domin suma su tsinki nasu `ya`yan itaciyar, kai ya ma tabbatar da cewa hatta majahidai na nan gaba suma sun halarci wannan nasarar domin ya kara karfafar su a kan wannan kuma ya hada zukatan su, kuma wadannan lamura ne wadanda da suke da kafa babba a cikin afladoniyya ta da da ta yanzu, wannan ne karshen maganar sa.
Bari in sanya wannan nassin a gaban mai karatu mai girma domin ya gani da kan sa, mene ne gwargwadon abin da yake na daidai daga cikin wadannan sakamakon wadanda Dakta ya fitar da kuma shaidun da ya jero da kuma fitar da ra'ayi irin na afladon din da ya ambata, sannan sai ya rufe maganar sa da abin da zai zo:
Na farko: Idan wannan nassin ya zo ne a kan raja'a to mene ne ma'anar cewa Imam Ali ne ya kirkiro akidar raja'a ba gullat ba kamar yadda Dakta kamila yake fadi.
Na biyu: Wannan nassin da dukkanin fahimta ta kusa- kusa bako ne kamar yadda Dakta yake fadi kuma ko kadan bai da sila da ma'anar da ya ambata, ko ma dai mene ne lalle wannan nassin abin da yake nunawa kuma yake nufi shi ne ruwayar nan da ta ke cewa: "Wanda ya so wasu mautane za a tashe shi a cikin su kuma zai yi tarayya da su a cikin ayyuakan su" don haka ne ma Imam Ali ya tambayi mutumin game da abin da zuciyar dau'uwan na sa take so, shin yana tare da amirnl muminina ne da sahabban sa? Sai ya amsa masa da na'am, sai ya ce lalle ya halarce mu. Ai ya yi tarayya da mu da shu'urin sa, sannan Imam ya ce da shi: Lalle baki dayan wadanda zamani zai rayu da su, wadanda mu a ra'ayin mu da sannu zasu yi musharaka da mu bayan haka a cikin samun lada da kuma farin cikin samun nasara, kuma misalsali da kwatamkwacin irin wadannan kalamai sun yawaita a cikin maganganun Imam sa, daga cikin wannan akwai abin da marubuta tarihin duffi suka ruwaito a in da suke cewa: Jabin bin Abdullahil Ansari ya ziyarci kabarin Imam Husain bayan kashe shi sai ya ce a cikin ziyara tasa: "Na shaida cewa mun yi tarayya da ku a cikin abin da kuke a kan sa" sai Rafi'atal A'amash ya ce: An yanke kawunan mutanen kuma sun yi jihadi har sai da aka ka she su, ta yaya muka zama mun yi tarayya da su a abin da suke cikin sa?" sai Jabir ya ce da shi "Lalle niyya ta da niyyar sahabbai na tana kan abin da Husain ya shude a kan sa da shi da sahabban sa" dukka nin ma'abota litattafan jiyarar Imam Husain sun ambaci wannan baki dayan su, wannan itace ma'anar maganar Imam Ali (a.s) ba kamar yadda Dakta ya tafi a kai ba.

Me Ye Matsayin Gullat
Barin in dan dawo baya kadan in dan nunawa ustaz Faragal wasu `yan ruwayoyi daga cikin makamantan su da daruruwan ire- iren sa, wadanda suke yin nuni a bisa inda gullatanci ya ke domin yasan cewa gullatanci yana wajen wasu ba Shi'a ba. Kuma ma bisa mafi munin tabbaci, a wajen Sunna akwai ninkin wanda ya ke wajen Shi'a, bari in fara masa tun daga kan halifanci in bi da shi bisa jeri daya bayan daya.
A- Sheda na farko: Shekh Ibrahim Al'abidi Almaliki (bamalike) ya ambata a cikin littafinsa Umddatut Tahkiki Fi Basha'iri Alis Siddik, ya ce an ruwaito cewa wata rana Manzo (s.a.w) ya ce da A'isha lalle Allah yayin da ya halicci rana ya halicce ta daga lu'ulu fari gwagwadon girman duniya sau dari da arba'in- tare da la'akari da cewa girman rana kamar yadda masana ilimin falaki suke cewa miliyan ne da dubu dari uku a gajeren takdiri, -kuma ya sanya ta a bisa sauri, kuma ya sanya saurin bisa igiya dari takwas da sittin kuma ya sanya sarkar yakutu ja a kowace igiya, sannan ya umarci mala'iku sittin daga cikin makisanta da su ja ta da wannan wadannan sarkokin da karfin su wanda Allah ya kebance su da shi, kuma rana kamar falaki ta ke a wajen wannan saurin kuma ita rana tana yin zagaye a cikin koren daki kuma kyan ta yana dada bayyana ga mutanen da suke doron kasa, kuma kullun tana tsayawa a kan madaidaicin zare (haddul istiwa'a) a sama Ka'aba saboda ita ce centar duniya:- a bin la'akari: Madaidaicin zare ba a kan Ka'aba yake ba- sannan kuma tana cewa: Ya mala'ikun ubangiji na lalle ina jin kunyar Allah Madaukaki idan na isa zuwa daura da saman Ka'aba, wacce itace alkiblar musulmi, kuma in wace tasaman ta, su kuma mala'iku suna jan rana da dukkanin karfin su domin ta tsallake saman Ka'aba, sai taki jawuwa mala'ilkui su kasa jan ta sai Allah ya yi wa rana wahayi ta hanyar ilhama sai su yi shela: Yake rana mun hada ki da girman mutumin da sunansa yake a rubuce a fuskarki mai haske, ki koma daga inda kika taho, idan ta ji haka sai ta motsa da ikon Allah, sai A'isha ta ce:
Ya manzon Allah wane ne mutumin da sunansa yake rubuce a jikin ta?
Shi ne Abubakar Siddik, yake A'isha tun kafin Allah ya hallici duniya ya sani da iliminsa maras farko cewa zai halicci iska kuma zai halicci wannan saman a kan iska kuma zai halicci kogi daga ruwa kuma zai halicci abin hawa mai sauri a kan ta saboda ranar da take haske duniya kuma yasan cewa rana zata yi wa mala'iku taurinn kai ya yinda ta isa zuwa tsakiyar duniya, kuma lalle Allah ya kaddara ya halicci wani Annabi a karshen zamani abin fifitawa a kan sauran annabawa kuma shi ne mijin ki, ya ke A'isha ko da makiya sun ki, sannan sai ya zana sunan wazirinsa ina nufin Abubakar Siddik abin zabi, don haka idan mala'iku suka roke ta da sunansa sai ta gushe ta koma daga inda ta fito da ikon Allah haka ma idan mai sabo daga cikin al'umma ta ya wuce ta wutar jahannama, sai ta yi kokarin ta kawowa mumini hari, saboda son Allah da yake cikin zuciyar sa da kuma sunansa da yake rubuce a harshen sa sai ta juya baya tana mai gudu.
B- Dalili na biyu: Muhammad dan Abdullahi Aljardani ya ambata a ciki littafinsa, misbahul zalama: An ruwaito daga dan Abbas cewa jibril ya zo sai ya ce ya Muhammad ka karanta gaisuwa zuwa Umar kuma ka gaya masa cewa yardar sa daukaka ce, kuma fushin sa hakuri ne, kuma lalle Musulumci zai yi kuku bayan mutuwar ka saboda mutuwar Umar, sai Manzo ya ce ya Jibril bani labnari abisa falalar Umar da kuma mmatsayin da yake da shi a wajen Allah madaukaki, sai ya ce: Ya Muhammad da zan zauna da kai gwargwadon yadda Annabi Nuhu ya rayu ba zan iya lissafa maka labarin falalar Umar da matsayin da ya ke da shi a wajen Allah ba,
C- Dalili na uku: Imam Ahmad dan Hambali ya fadi a cikin musnadinsa da isnadinsa daga A'isha, cewa lalle Abubakar ya nemi izinin shiga wajen Manzo Allah (s.a.w) a lokacin da ya kasance a kishingide a cikin dakin sa cinyoyin sa a waje tare da kwaurikan sa, sai Abubakar ya nemi izinin shigowa sai ya yi masa izini sai suka yi hira sai Umar ya nemi izini sai ya yi masa izini ya shigo Manzo yana yadda yake bai canja ba, sannan sai Usman ya nemi izini sai Manzo ya daidai ta zaman sa sannan sai ya daidata tufafin sa sai A'isha ta ce: Abubakar ya shigo ba ka ji kunyar sa ba kuma ba ka kula da shi ba, sannan Umar ya shigo ba ka ji kunyarsa ba, kuma ba ka kula da shi ba, sannan da Usman ya shigo sai ka zauna sannan kuma ka daidaita zamanka. Sai Manzo (s.a.w) ya ce ashe ba na ji kunyar mutumin da mala'iku suke jin kunyar sa ba.
Wadannan su ne misalsali guda uku daga cikin gomomin irin su wadanda su kan su halifofin ba su yarda da ita ba, suna da muwafakat da cewa da darajojin da suka ishe su, su ba su bukatuwar yayime-yayime da haniniyar sakarci, kamar yadda tarihin Musulumci, shi yafi girma fiye da mu yarda mu zama abin da za a rika yin amfani da shi wajen cenja tarihi. Cikin abin da tahirnmu ya tattaro akwai abubuwan da suka isar wajen tabbatar da daukakar Danadamtaka, domin in bi bayan wadannan ruwayoyin, barin in cito maka wadannan ruwayoyin, da wasu misalsalin na daban wadanda rigimar mazhabci ta haifar da su, kuma ba tare da ya kula ba sai gashi ya zubar da kimar mazhabar baki daya. Inbul jauziyya yana fadi a cikin littaifnn sa Yakut: Abuhanifa a lokacin rayuwarsa ya san Annabi Hidhir kuma lokacin da ya mutu Hidhir ya yi bakin cikin rasa shi, kuma ya yi munajati da Ubangijinsa ya ce da shi, ya Ubangiji na idan har ina da matsayi a wajen ka, ka yi wa Abuhanifa izini ya ilimantar dani alhali yana cikin kabari, kamar yadda yakance yana yi da har sai nasan shari'ar Muhammad a kammale, sai Allah madaukaki ya raya shi sannan ya nemi ilimi a wajen sa har tsawon shekara ishirin da biyar….h.i.k. to wa ke nan ya tafi a kan raja'a ya ku Musulmai?.
Kuma Ibnul Jauziyya ya na cewa a cikin littafin, Manakib daga Ali dan Isama'il, ya ce; na ga tashin alkiyama, sai mutane suka zo wajen wata gada, ba a bari koya ya wuce sai ya zo da sutamfin (sheda ko alama) daga wani mutum da yake zaune a gefe yana yi wa muytane stamfi, yana ba su sai na ce waye wancen sai aka ce Ahmad dan Hambali ne.
Ya isar maka ka karanta ruwaya a kan Imam Malik da Imam Shafi'i da ma da yawa daga cikin fakihai, da Imamai na daga abin da son rai ya sako, sannan kuma aka sa a gaban mai karatu, na daga abin da yake cutar da kwadayin sa kuma ya ke kuntata yadda yake ihsasi (ji). Sannan kuma bayan haka me za a kira misalin irin wannan shin guluyyi ne ko kuma ba wata tambaya da za a fuskantar zuwa ga Ustaz Faragal! da sannau zan bawa Faragal wani misali guda daya kawai, mai tafsirin ruhul bayan yana cewa:
A yayin da yazo kan fassarar (A wannan ranar guda takwas ne suke rike da al'arshin ubangijin ka) lalle rabin wadanda Allah ya fadi a cikin wannan ayar su ne Abuhanifa da Malik da Shafi'I da Ahmad dan Hanbal??!!.
Haidar Center for Islamic Propagation
Face Book: Haidar Center
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Monday, December 10, 2012

comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.