Ismar Wasiyyan Annabi

Ismar Wasiyyan Annabi

Related ArticlesIsmar Wasiyyan Annabi

SHEIKH WA'ILI
Fasali Na Uku
Saboda Me Aka Danganta Shi'a Da Abdullahi dan Saba'
A wajen amsa wannan tambayar ne babbar manufar wannan kissar gabaki dayan ta yake boyuwa, kakika tunanin shi'anci a kan imamanci da abin da yake danfare da ita da kuma matsayan da a ka sajjalawa (bawa) Shi'a a tsakanin bangarorin Musulmai na daga Shi'a da wasun su, idan ka koma zuwa tushen su, daga dalilan sa na Kur'ani da hadidi ta yiwu sama kasa ta koma sama, saboda lamarin wasici da isma da makamancin su sun wuce lamarin shugabancin- a mahangar Shi'a- ga wanda bai cika wadannan sharadan ba kuma wannan ita ce babbar musiba, kuma wane tunani ne yafi hadari fiye da wannan, don me kuwa ba za a gwama tushen Shi'a da na Yahudawa ba, a kuma kirkiro masa mutum-mutumi a matsayin ragon layya, sai a samu damar jefa wa Shi'a zargi, da wadanda suka rika daga gareta, kuma a rika nuna su da cewa su fitattu ne daga Musulumci, wadanda suka bata tatihin al'umma kuma suka dasa akidu sababbi wadanda ba na Musulumci ba a cikin akidun ta, kuma haka Abdullahi dan Saba' ya aikata, da a ce da gaske ne ya aikata hakan! duk da cewa hankula da ma'aunai ba su yarda da faruwar hakan ba.
Kari a kan abin da muka ambata, akwai wani sababin na daban da ya sa aka halicci Abdullahi dan Saba' wanda Dakta Ahmad mahmud Subhi ya yi nuni zuwa gare shi, wannan kuwa bayan da ya bijiro da ra'ayin Daha Husain a yayin da ya yi nuni zuwa wahamcin samuwar Abdullahi dan Saba', Dakta Ahmad Subhi ya ce:
Da alamun cewa lalle kai mutukar malaman tarihi da marubutan mazhabobi a kan hakikanin abubuwan da dan saba' ya aikata yana komawa ne zuwa wani sababi na daban wanin wanda Dakta Daha Husain ya ambata, kakika abubuwa na siyasa manya- manya sun faru a Musulumci kamar kashe Usman, sannan yakin Jamal, kuma lalle manya- manyan sahabbai sun yi musharaka a cikin su haka matar Manzo (s.a.w) kuma dukkanin su sun rarraba su na yakar juna, kuma dukkanin wadannan fare- faren suna cin karo da (wujdanin) shu'urin ko gamsuwar musulmin da yake biye da tarihin sa na siyasa, ya zama an jarrabci Musulumci irin wannan jarrabar kuma manyan- manyan sahabban da suka yi yaki tare da Manzo (s.a.w) kuma sukayi tarayya a wajen kafa Musulumci, babu makawa zai dora nauyin faruwar wannan abubuwan a kan wuyan wani, kuma baya daga cikin abin da hankali zai karba a dora nauyin wadannan fare-faren ga bakidaya a kan manya- manyan sahabban wadanda suka yi bala'i kyakykyawa. Don haka sai ya zama babu makawa ya dora nauyin wannan lamarin gaba daya a wuyan dan Saba', don haka ke nan shi ne wanda ya tada fitinar da ta kai ga kashe Usman kuma shi ne ya harzuka rundunoni guda biyu a ranar jamal domin su gamu a lokacin da Ali da Dalhatu da Zubair suke a gafale, amma a cikin tarihin da tunani yake rike da shi, shi ne cewa a wuyan sa ne mafi girma rarrabar akidun Musulumci ya doru ta hanyar bayyanar Shi'a, wannan ita ce fassasrar ta kai mutukar da marubutan firkoki da masu mazhabibi suka yi, musamman ma salafiyyawa da masu tarihi: A bisa hakikanin rawar da Abdullahi dan Saba' ya taka. Sai dai a she ba abin ban mamaki ba ne, wanda ya sabon-shiga cikin Musulumci ya yi abin da yake so kamar haka ba, ya motsa tarihin Musulumci na siyasa da na akida bisa yanayin da ya tabbata alhali manya- manyan sahabbai suna gani
Bayan wannan masaninyar a kan rudanin lamarin Abdullahi dan Saba' wanda muka kare gama a kai, bari mu yi gaba domin mukamo zaren ta daya bangaren bisa ga abin da muke tsammanin, wanda shi ne danganta akidar Shi'a da Abdullahi dan Saba' da kuma abin da suka jingina izuwz gare shi na daga akidun Shi'a domin mu nemi sanin asalinta a musulunci, da haka ne zamu magance dagewa a kan samuwar dan Saba' ko kuma rashin samuwar sa domin ya tabbata cewa lalle wannan akidar asalin ta daga Musulumci ne, sai ya zama babu wata kima bayan haka da zata yi saura a kan rashin samuwar dan Saba' ko samuwar sa, bari mu fara tabbatar da hakan daga maudu'in wasiyya.
1- Imam Ali Wasiyyin Annbi Ne:
Mun riga mun fadi a abin da ya gabata cewa yana daga cikin hukunce- hukuncen Musulumci mutum ya yi wasici kafin mutuwar sa da abin da yake son yin tasarrufi a cikin sa bayan mutuwar sa a cikin abin da ya mallaka na daga kayayyakinn rayuwa, kuma mun ambaci cewa lalle a rayuwar Manzo (s.a.w) ya kasance ba ya fita daga madina domin yin wata tafiya koda ta kwana daya ce, face sai ya sanya halifa a madina. Ta yaya zai bar lamarin wannan al'ummar kara zube a bayan sa, ya sanya ta a cikin rudani ba tare da ya yi wasici ko ya zabi mutumin da zai tafiyar da lamari a bayan sa ba, gama cewa lalle wannan matsalar tuni alkaluman marubuta suka gamsar ta ita daga mabanbantabn bangarori bana so in dawo zuwa abin da ya gudana a kan ta abin da ya ke gaban mu a nan shi ne mu bayyana cewa mas'alar wasiyya ta samo asali ne daga Kur'ani da Sunna. Amma Kur'ani ya sanya Ali abokin tarayya a cikin lamarin shugabanci na baki daya kuma ya sanya imamancinsa ci gaba ga isar da sakon Allah tun da an riga an kulle annabtaka daga lokacin da Manzo ya rasu.
Allah Madaukaki ya ce: "Kadai waliyyin (shugaban ku shi ne Allah da Manzonsa da wadanda suka yi imani wadannan da suke tsaida salla kuma suke bada zakka alhali suna cikin ruku'u". Kuma lalle mun ambaci yadda wannan ayar ta sauka akan Ali da kuma abin da yake damfare da ita na daga lazimce-lazimce a wani wajen a cikin wannan littafin. Amma Sunna madaukakiya kuwa akwai ruwayoyi managarta masu yawa da suka bayyana cewa lalle Manzo (s.a.w) ya yi nassi da wasicin Ali a mafi yawan warare, daga cikin wuraren akwai:
Yayin da ayar "Ka gargadi `yan'uwan ka makusanta" shura'a /214 ta sauka, sai ya tara makusantansa, su arbain ya tanadar musu cinyar akuya sannan ya nemi su wazirce shi a kan lamarin kira zuwa ga Allah, alokacin ba wanda ya tashi sai Ali, sai ya riki wuyan sa ya ce wannan ne dan'uwana kuma wasiyyi na kuma halifa na a cikin ku, ku ji daga gare shi ku bi. Sai mutanen suka ta shi suna dariya suna cewa da Abi Dalib: Ya umarce ka, ka ji daga danka kuma ka bi.
Kuma Ibn Abil Hadid a cikin littafinsa sharhin Nahjul balaga ya yi fasali guda gamsasshe a kan lamarin wasicin Imam Ali (a.s) daga Annabi (S.AW.) kuma ya kosar da wannan maudu'in, kuma mai karatu zai iya komawa gare shi. A yanzu dai ka riga ka ji cewa wasiyya ta gudana ta harshen Manzo (s.a.w) bisa lafazin ta da ma'anar ta, tare da haka zaka ga wadannan mutanen suna cewa lalle maudu'in wasiyya Abdullahi dan Saba' ne ya kirkiro shi, kuma da sannnan zaka ji- da zaka ce musu lalle wasiyya tana da masdarin ta (asalin ta) a Sunna- wanda zai ce maka wadannan hadisai ne da Shi'a suka dasa su ta harshen Sunna.
2- Isma (Rashin yin Sabo da Kuskure)
Lamarin isma lamari ne mai mihimmancin gaske musamman a mahangar Shi'a, dama Musulumci baki daya, don haka ya zame mini larura in tsawaita a kan sa saboda tana damfare da abubuwa masu mihimmancin da babu makawa da mu yi bayanin su (a sansu).
Isma dai a luga: Ita ce tsaruwa, daga wannan ne fadinsa madaukaki "Da sannu zan fake zuwa dutse, zai tsare ni daga ruwa" surar hudu/43. Amma a isdilahi malaman akida: kuma, ludufi ce da Allah Madaukaki yake ba da shi ga baligi ta yadda zai zama bashi da wata dama ta barin bin Allah da kuma yin sabo tare da ikon sa a kan hakan.
Mafi fitowa sarari daga wannan ta'arifin shi ne cewa lalle isma babu jingino a cikin ta, ba komai ba ce face sai kama hannu daga wajen Allah da kuma tanadi daga bawa. Don haka tafi kama da a ce malami ya kula da dalibin sa saboda ya sami shi wanda yake da cikakken iko wajen karbar ilimi sama da waninsa.
Kuma lalle al'umma ta hadu a kan ismar Annabawa daga ganganta karya a cikin abin da suke isarwa daga Allah Madaukaki bayan haka kuma sun saba akan yiwuwar ya aikata abin da ya ke kore isma bisa rabkanuwa ko mantuwa, daidai ne dalilan su a cikin wannan sn kasance na ji da kunne ko kuma na hankali, a bisa zuwa ko rashin zuwa da abin da yake kore isma, sashin malaman Ahlus-sunna sun tafi a kan halaccin faruwar kowane zunubi daga gare su, karami ne ya kasance ko babba kai har ma kafirci, kuma mai karatu zai iya komawa zuwa ra'ayiyin Bakalani da Razi da Gazali a kan ra'ayin imamanci dalla-dalla, a yayin da wasu kuma suka yi fasali a kan hakan amma ba su kai zuwa ga wannan iyakar ba, a wajen wofintar da su daga isma.
Amma Shi'a sun tafi a kan ismar Annabawa kai tsaye kafin aiko su da bauann sa, kuma sun zo da dalilai masu yawa a kan hakan. Fakhrur Razi a cikin littafinsa Ismatul Anbiya'i, ya bijiro da lamarin, haka ma Shekh Majlisi a cikin Biharu ya zo da shi dalla-dalla, abin da ya ke gaba na anan ismar Imamai domin shi ne mahallin bahasi na, lalle ismar annabawa abu ne wanda yake tabbatacce a wajen Shi'a kuma Shi'a sun tabbatar da ita ga Imami da dalilai na hankali da na ruwaya zan takaita wajen ambatar wasun su kuma wanda yake neman kari zai iya komawa zuwa litattafai da kuma manya- manyan litattafai da suke magana a kan wannan.
?
Ismar Annabawa Da Dalilanta Na Hankali
Dalili Na Farko:
Allma Hilli yana cewa a cikin littafain sa Al'alfain: Samammu cikin samuwar su da rashin samuwar su suna bukatar mai samar da su wanda ba irin jinsin su ba domin da zai kasance daga jinsin su, da zasu bukaci wani mai samarwar daban wanda samuwar sa ta tsayu da shi kan- kan sa (wanda ya dogara da kan sa), kuma wanda ba samar da shi aka yi ba, kuma samun kuskure daga dan Adam abu ne mai yiwuwa, idan kuma muka so mukawar da kuskure daga abin samarwa ya zama wajibi mukoma zuwa wanda ya wofin ta daga sabo wanda shi ne Ma'asumi, kuma ba zai yiwu mu kaddara rashin ismar sa ba saboda zai kai mu ga tasalsul ko dauri, amma tasalsuli, lalle idan Imami bai zamo Ma'sumi ba zai bukatu zuwa wani Imamin daban, domin dalilin da ya bukatar da samuwar sa shi ne, halarcin yin kuskuren mutane, don haka da yin kuskure zai halatta a gare shi to da ya bukaci wani Imamin daban, idan ya zamo na biyun ya zama ma'asumi to! In ba haka ba wannan zai lazimta mana tasalsuli. Amma dauri saboda bukatuwa zuwa Imami, da bai zamo Ma'asumi ga mutane ba da ya yi kaikawo a kan daidai, tare da bukatuwar mutane zuwa yin koyi da shi.
Dalili Na Biyu
Shi'a suna cewa: Lalle ma'anar Imami ta tattaro ma'anar isma, domin Imami a luga shi ne wanda ake yin koyi da shi: Kamar (misalin), mayafi suna ne abin da ake yafawa, da ya halallta ga Imami ya yi zunubi, a yayin da ya yi zunubi, ko dai a yi koyi da shi ko kuma kada a yi, idan na farko ne to ke nan Allah Madaukaki ya yi umarni da a yi zunubi, wannan kuma korarre ne, idan kuma na biyun ne imamin ya fita daga kasancewar sa Imami, kuma kawar da tanakudi tsakakin wajabcin kasancewar sa wanda za a yi koyi da shi, da kuma wajabcin yin umarni da kyakykyawa da yin hani daga mummuna abu ne dab a zai yiwu ba, sai dai in za a yi tasauwurin cewa lalle isma tana cikin mafhumin imamanci kuma ta lazimci samuwar sa.
Dalili Na Uku
Imami hujjar Allah ne a wajen isar da sakon shari'a ga bayi kuma shi ba kawai yana kusantar da bayi zuwa yin biyayya kadai ba ne, sannan ya nisantar da su daga sabo ta bangaren kasancewar sa mutum ba ne kadai, ba kuma don yana shugaba ba, domin sashin shuwagabannin da suka yi da'awar Imamanci sun kasance fajiran da bai halatta a yi koyi da su ba , idan suka yi umarni da a yi biyayya ga Allah sun zama matabbatar fadin Allah Madaukaki:"Shi kwa yi umarni da kyakykyawa sannan ku manta da kanku" surar Bakara/44.
A irin wannan yanayin baligi ba zai amintu da maganar su ba kuma yana da uzuri, ka ga ya tabbata ke nan don a kusanta mutane da Allah ne ba kawai don Imami yana Imami ba, kadai yana zamowa ma'asumi ne domin kada mutane su zama suna da uzurin saba masa, domin gasgatawa ga fafin Allah Madaukaki "domin kada mutane su zama suna da uzuri akan Allah bayan aiko manzanni". Surar Nisa'i/165. Kuma Imamai hujjojin Allah ne kamar dai manzanni daidai- wa- daidai domin Allah ne ya nada Imami domin ya shiryar da mutane.
Wadannan dalilai guda uku ke nan daga cikin da yawa daga dalilan hankali wadanda suka dogara da su wajen kafa hujja da dalili a kan Isma.
?
Hujjojin Nakali Kan Ismar Imami
A. Allah madaukaki a cikin surar Bakara aya ta 124 ya ce da Annabin sa Annabi Ibrahim: "lalle zan sanya ka Imami a doron kasa, sai ya ce haka ma daga cikin zuriya ta sai ya ce azzalumai ba za su rabauta da wannan alkawarin nawa ba". Wannan ayar ta yi nuni a kan isma domin mai yin sabo azzalumi ne, ko da kuwa a kan kan sa ne. saboda fadinsa madaukaki "daga cikin su akwai wanda yake zaluntar kansa"32/fadiri.
B. Allah Madaukaki ya ce:"Ya ku wadanda kuka yi imani ku bi Allah da Manzo da shuwagabanni daga cikin ku"49/Nisa'i. A nan hujjar da ke kunshe a cikin wannan ayar ita ce cewa ma'abota al'amarin da ya wajaba a bi su, wajibi ne umarnin su ya zama daidai da hukunce-hukuncen Allah Madaukaki, domin ainihin wannan biyayyar ta zama wajiba a gare su, kuma hakan ba zai taba samuwa ba sai in suna da isma, domin da kuskure zai gangaro daga gare su to da ya zama wajibi a musanta musu wannan kuma yin hakan ya ci karo da umarnin Allah Madaukaki na cewa a yi musu biyayya.
C. Aya ta talatin da biyu ta surar Ahzab da ta sauka a kan Ahlul-baiti tana baya ni ne, a kan ismar su, ita ce: "Lalle Allah yana so ya tafiyar da dauda daga gare ku ya ku `ya`yan gida (na Manzo) kuma ya tsarkake ku tsarkakewa". Bayan ya tabbabta cewa ta sauka a kan Ahlulbaitn da kowanne daga cikin Imam Ahmad Bin Hambali a musnadinsa da Musatadrakus Sahihaini da Durrul Masur da Kanzul ummal da Sunanu Turmuzi, da Tafsirul dabari da Khasa'isul Nisa'i da Tarihi Bagdad, da Istii'ab na Ibn Abdul Bar da Riyadhun Nadhra na Muhibbul Din Addabari da Musnadi Abu Dauda da Usudul gaba, suka zo da nassi a kan su. Kuma dukkanin su sun ce ta sauka a kan Annabi (s.a.w) da Ali (a.s) da Fadima da Hasan da Husain (a.s).
Kuma malamai na ta sa alamar tambaya a kan ma'anar gusar da najasa? domin su tuke zuwa cewa ana nufin kore kowane irin zunubi da kuskure daga garesu kuma irada anan takwiniya (ta halitta) ce ba ta shari'a ba ce, saboda a sarari yake cewa irada ta shari'a dukkanin mutane sun yi tarayya a cikin ta. Kuma bai zama yiwu a gare shi ya jingina da abin da muka fadi a baya ba na cewa lalle isma gudun mawa ce daga Allah da kuma tanadi da dagewa daga bawa ba. Wadannan su ne sashin dalilan Shi'a a kan isma, kuma kamar yadda kake gani dukkanin su an ciro su ne daga Kur'ani da Sunna da kuma hankali, ta wace fuska za a iya jingina wannan da Abdullahi dan Saba'? ina mahallin gasgata wannan daga waccen dangantakar. Lalle mai karatu yana da hakkin ya tambayi wadannan marubutan cewa shin sun leka masdarorin akidar Shi'a a lokacin da su ke yin rubutu a kan ta, ko kuwa, idan har ta farkon ce amsar ta me kuma ya kawo wannan gutsuri tsamar da wannan kuskurarriyan dandantakar, idan kuma ta biyu ce daidai, to mai ya kai su ga yin ruko da abin da ba su da tsinkaye a cikin sa, ashe yanzu ba suda mai tsawatarwa daga cikin ladubba na kyawawan dabi'ar koyarwar Musuluncin da Allah Madaukaki ya tsara a cikin fadinsa: "kada ka tsaya a kan abin da ba ka da ilimi a kan sa lalle ji da gani da zuciya dukkkanin su abababan tambaya ne a kan sa" isra'i/36 a lokaci guda kuma, tafarkin da tsarin koyarwa da amana ta ilimi ta ki ta yardar musu da wannan kage-kagen da kuma dangana abu zuwa ga wanin masdarinsa, idan haka ne ke nan, koda kuwa dalilan lamarin isma ba su zam karbabbu ba, to bai halatta ba a nisanta ta daga masadarin ta zuwa wani mutum na daban wanda gaba da kiyayya ta haifo shi kuma son rai ya fitar da ayyukan sa a fili ba.
Matsayar Sunna a kan Isma
Kafin mu shiga cikin maudu'in namu zan dan waiwayar da mu zuwa wata kissa wacce ta ke ita ma tana dauke da ta ta manuniyar a kan wannan maudu'in, ita ce: An kai wani mutum da ake bin sa bashi wajen alkali, sai alkalinn ya tambaye shi: Shin wannan mutumin da ya kawo karar ka yana binka bashi ? sai ya ce a yanan bi na bashi amma ban yarda da yana bi na ba, wannan kissar ta yi kama da wanda yake musanta mana isma kuma a lokaci guda sai kuma ka ga ya na da'awarta.
Tare da cewa muna sanya sharadin isma ne ga Imami domin tabbatar da cikakken tsaro da kariya domin isuwar hukunce- hukunce da akidu zuwa hannun mu ingantattu. Kuma da tabbatar da nisanta daga rarraba wacce take faruwa saboda kasantuwar shagaba ba ma'asumi ba ne, ba muna so isma ta zama wani daukaka ce da muke dorawa a kan wuyan imamai ba ne, suna da falalolin da sun ishe su daga wannan, kamar yadda ba mu kasance masu yin linkaya a cikin kogin jin fifici da jin cewa mun tsira ba, sam-sam domin kawai muna son yin ko wani abu bisa yadda yake, mu kuma raya duniyar dare da dukkanin bambamce-bambancen ta, lalle a kan maganar imamanci mun barranta da mu zamo wadanda su ke ganin kasantuwar Imami daga cikin wadanda muke ganin su daga mutane kawai, domin idan suka zamo da irn wannan yanayin da tsarin, to mene ne bambancin kuma da me suka zama zababbu har sa zamo masu yin hukunci a kan mutane, alhali a cikin mutanen akwai wadanda suka fi su tsayuwa da dagewa da cencneta. Wadannan su ne abubuwan da muke nufatan abayan isma, ba wai isma wata aba ce ta daban ba wacce ba ta dan Adamtaka ba, kamar yadda wasu su ke surantawa. Isma a mahangar mu nagarta ce da ke sawa a kiyaye shari'ar Allah Madaukaki nazarce da kuma kiyaye ta daga wasanni a aikace, kuma manya-manyan malaman Sunna sun tafi a kan haka, a lokaci guda kuma suna musanta mana yin riko da ita, kuma ga ma wasu misalsali daga maganganun su domin ma kasan ingancin abin da muka nasabta musu.
Arrazi: Yayin da Razi zo yi wa Shi'a raddi a kan ismar Imamai, sai ya tafi a kan cewa: Babu bukata zuwa Imami ma'asumi, domin al'umma yayin da ta hadu zata zama abar tsarewa (ma'sumiya) saboda dafifi da haduwar al'umma a kan kuskure, bisa fadin Manzon Allah (s.a.w) abu ne mai yiwuwa . "Al'umma ta ba zata hadu a kan bata ba".
Idan muka rufe idon mu daga kallon ingancin wannan hadisin ko rashin ingancin sa, sai mu yi tambaya, shin irin wannan ijma'in abu ne mai yiwuwa ta yadda zamu game dukkanin musulmi na gabas da na kudu? Ta yiwu a ce musulmin da suke kamantawa wannan ijma'in sune ma'abota warwarewa da kullawa ne, sai mu yi tambaya su wane ne kuma nawa ne adadinsu, kuma shin an taskace su a wani wuri ne? Kuma meye dalili a bisa hakan? Sannan mu kuma yi tambaya: Ashe ba komai ake nufi da haduwar ta su face sai hada su daya bayan dayan ba, idan har zai yiwu dayan su ya yi kuskure, zai yiwu dukkanin wadanda suka hadu a daidaikunsu su yi kuskure. Lalle Ibn Taimiyya ya amsa wannan tambayar da cewa, bai zama lazimi gaba dayansu su yi kuskure ba domin tarayya tana kebance- kebancen da ba a samu a daidaiku.
Kuma misalin wannan kamar misalin loma daya ce wacce ba ta kosarwa a yayin da da waya suke kosarwa, kuma sanda daya tana karyuwa a yayin da da yawa ba sa karyuwa har dai zuwa inda ya ce Manzo (s.a.w) ya ce: Shaidan yana tare da mutum daya kuma yafi nisanta daga mutum biyu , ban sani ba ta wace fuska za a kamanta tsakanin kasantuwar lomomi suna kosarwa da kuma kasantuwar daya bata kosarwa da kuma tsakanin kasancewar tarayya tana kaiwa ga isma da kuma rashin tsaruwar mutun daya, domin loma tana dauke da yiwuwar ta kosar da wani bangare ayyanan ne ta yadda idan ka kara wata a kan ta sai tarayyar wadannan daidaikun lomomin su hadu su bada koshi cikakke, haka ma sanda tana dauke da wani gwargwado na karfi, idan ta hadu da wasunta sai ta ba da cikakken karfi, miye alakar wannan da mutum daya wanda yake iya yin kuskure? Ba zai iya zama wani bangare na inganci ba ta yadda idan a kan hada shi da wasun sa zai zama ciko na inganci ba, balle ma zai ba da akasin sakamakon da ake bukata ne, domin mutum daya a nan yana kamanta rinjayen masu kuskure ne, ta yadda idan aka hada shi da misalin sa, sai kuskuren ya rubanya sai ya zama babban kuskure, lalle wannan kiyasi ne tare da mararrabiya a tsakani, wannan ta wani bangaren ke nan.
Ta wani bangaren kuma, lalle Ibn Taimiyya bai kore tunanin imamanci ba kadai, ya kore kasantuwar ta a kan mutum daya ne kawai, kai ka ce yana jin haushin ta kasance ga mutum daya ne, amma da za a danganta ta ga wasu mutane to ba komai, ta bangare na uku kuma, kadai an shardanta isma ne ga al'umma domin a sami sikka da kuma tabbatar da amintar hukunce-hukunce wanda shi ne ainihin hadafin da Shi'a suka tafi a kan sa, kuma yanzu zan cirato maka ra'ayin sa dalla-dalla:

Ra'ayin Dan Taimiyya a Kan Isma
Ibn Taimiyya a yayin da ya ke yi wa Shi'a raddi a kan fadin su: Lalle samuwar Imami ma'asumi abu ne da babu makawa da shi bayan wafatin Manzo (s.a.w) saboda hukunce- hukunce suna sabuntuwa da daidai da yanayi, kuma yanayoyi suna cenjawa, kuma domin kada a samu sabani a cikin fassara Kur'ani da kuma fahimtar Sunna, kuma da a ce ismar Manzo da kuma cika wannan addinin sun isar da ba a samu sabani ba, sai ya tabbata cewa babu makawa da samun Imami ma'asumi wanda zai bayyana mana ma'anonin Kur'ani ya kuma ayyana mana manufoffin shari'a kamar yadda dama wannan ne abin da aka nuface shi da shi, har dai zuwa abin da aka ambata zuwa karshen abin da suka ambata a wannan matsayar.
Ibn Taimiyya ya ce: Ahlus-sunna ba za su sallama a ce Imami ya zama shi ne zai kiyaye shari'a bayan yankewar wahayi ba, domin wannan ya hau kan kowa ne, ka ga shiri'a, idan har mutane da yawa suka ciro ta, hakan yafi fiye da ciratowar mutum daya, ka ga makaranta ma'asumai ne a wajen hardace Kur'ani da kuma isar da shi, kuma masu hadisai ma'asumai ne a wajen kiyaye hadisai da da kuma isar da shi, kuma fakihai ma'asumai ne a wajen yin magana da kuma kafa hujja , kuma Ibn Taimiyya ya saba da Razi a nan, idan har isma a wajen Razi tana tabbata ne da haduwar al'umma, to a wajen Ibn Taimiyya tana tabbata ne ga wasu jama'a ne daga mutane kamar makaranta da fakihai da masu hadisai, kuma a nan IbnTaimiya ya shardanta isma domin tabbatar da kiyaye abin da shari'a ta kunsa kamar dai yadda yake a wajen Shi'a da wasun su, to don me zai halar ta ga wasu sannan ya haramta ta ga wani? Adadin ma'asumai a wajen Shi'a bai wuce goma sha hudu ba, kuma su ne tarayyar zababbun mutanen da Allah ya kebance su da falaloli masu yawa bisa ijma'in bangarorin Musulmai, to don me muke musanta musu isma sannan kuma mu halartata ga wasun su?

Ra'ayin malaman Sunna a Kan Isma
Za mu iya cewa jamhurun malaman sannan sun tafi a kan ingancin hadisin da aka ruwaito daga Manzo (s.a.w) "sahabbai na kamar taurari ne duk wanda ku ka yi koyi da shi kun shiriya " kuma wannan hadisin ya lazimtar da ismar sahabai kamar yadda wannan bayanin zai zo daga sashin su, domin ingancin yin koyi da su da kuma yi masa biyayya a cikin zalunci da zai faru saboda kasancewar sa wanda yake aikata zunubai kuma wannan shi ne abin da ya faru saboda kasantuwar su ba ma'asumai ba ne, wannan yana nufin ke nan Allah ya yi umarni da abi mai sabo da kuma yin zalunci ko da kuwa a kan sa ne, idan kuma bai yi aiki da abin da Manzo ya ce ba, wannan yana nufin ya saba wa Kur'ani ke nan: "Abin da Manzo yazo muku da shi ku yi riko da shi" .
A nan kuma sahabi yana cirato umarnin Manzo idan ka ce lalle Allah Madaukaki ya umarce mu, ida ka ce lalle Manzo ya yi umarni da mukarbi hadisi daga adali sikka saboda fadinsa madaukakin: "Ya ku wadanda suka yi imani idan fasiki ya zo muku da labari ku yi bincike don kada ku auka wa mutane bisa jahilci". Hujurat: 6. Wacce bisa abin da a ke fahimta daga wannan ayar cewa labarin (adali) amintacce hujja ne kuma mu ba ma karbar umarni sai daga adali daga cikin su. Sai na ce :Lalle wannan yana yin nuni a bisa cewa a cikin su akwai wanda ba adali ba kuma wannan ne abin da muke son tabbatarwa.
A dunkule lalle lazimin wannan hadisin da aka ambata shi ne ismar sahabbai, kuma ba mu ji wanda yake musawa wadannan ba, to don me idan Shi'a sun ce imamai ma'asumai ne ake yi musu nakadi?.
Tafatazani Da Isma
Tafazani wanda yana daga cikin manyan malamai yana cewa a cikin littafinsa Sharhil Makasid: Mutanenmu sun kafa hujja a kan rashin wajabcin isma bisa ijma'i a kan imamancin Abubakar da Umar da Usman, tare da ijma'i a kan cewa bai zama wajibi su zama ma'asumai ba, duk da cewa sun kasance ma'asumai a bisa ma'anar cewa tun lokacin da suka yi imani sun kasance suna da dabi'ar nisantar sabo tare da ikon yin su !.
1- A nan Tafazani yana tabbatar da ismar halifofi guda uku
2- Yana cewa: Lalle ismar su ba wajiba ba ce, da nufin cewa ba a tilasta musu a kan ta ba in ba haka ba ba zai yiwu ba a sauwara ratayar hukunce- hukunce da lamurrann halitta ba, kadai an halicce su da cikkken zabi da tanadi na su zam ma'asumai a fagen hukunce- hukuncen ayyyuka da motsin yau da na gobe.
3- Abin da yake nufi da cewa isma malaka ce da take hana mai ita yin zunubi, ba bisa yanayin kwace zabi ba, kuma wannan shi ne ainihin abin da Shi'a suke fadi a cikin imamai kuma duk wanda yake so ya koma litattafan Shi'a na akida a kan bahasin isma, bayan wannan kuma don me a ke ta wannan iface-ifacen yak u masaumai.

Shamsuddin Al'isfahani Da Nur Muhammad A kan Isma
Hafiz Nur Muhammad da Shamsudddin al'isfahani na farko a cikin tarihin maziyarta madaukakiya, na biyu kuma kamar yadda algadir ya nakalto daga gare shi cewa: Lalle halifa Usman ma'asumi ne , kuma ya nakalto shi ne daga littafinsa madali'il Anzar kuma wadanann mutanen biyu daga malaman Ahlus-sunna ne.
Sheikh Iji Da Isma
Adurrahmanil ijabi ma'abocin littafin almawakif a cikin shi wannan littafin ya tafi a kan cewa ismar halifofi bisa yanayin da tafzazi ya fadi a cikin abin da muka ambata a kan sa na cewa lalle ita mallaka ce a gare su wacce bata tabbatar da sance zabi , kuma shi ma yana daga cikin malaman Sunna, kuma lalle wannan zagayen (jaular) ta bayyana mana cewa ba su ne kadai suka tafi a kan isma ba, ballatana ma malaman Sunna ma sun tafi a kan hakan, in haka ne ta wace fuska za a jingina ta Abdullahi dan Saba', kuma ta wane bangaren za a yi wa shia'a nakadi a kan yin riko da ita.
Ba ina so in sokarwa mai karatu litattafa da wallafe-wallafen Ahlus-sunna ba ne, kakika litattafan su cike suke da wannan, amma zan dan bijiro da ra'ayin wani marubucin karni na ishirin kuma a cikin wannan lokacin da duniya ta zama gari daya, shi kam na rantse da Allah yana daga cikin mafi yawa yin adalci wajen yin rubutu a kan Shi'a, amma duk da haka abubuwan da aka kafa a cikin zukata sai da suka yi saura suna ta yin aikin su.
Na yi imani cewa wannan mutumin ya yi bincike a cikin litattafan Shi'a da ma na wasun su kafin ya rubuta wannan littafin nasa wannan kuwa saboda abin da na gani a tatter da shi n masdarori masu yawa, tare da kaddara cewa ya leka ra'ayoyin Ahlus-sunna a kan a wadannan maudu'an, to don me za a musantawa Shi'a su kadai banda wasun su, idan kuma har bai karanta ba (leka ba), -kuma wannan ne abin da nake kore faruwarsa-, don me zai yi rubutu a kai?.
Haidar Center for Islamic Propagation
Face Book: Haidar Center
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Monday, December 10, 2012

comments

Leave a Comment

* Filayen alama tare da wani alama dole ne, haƙĩƙa, da darajar.